Kotu ta ƙalubalanci hukumar ‘yan sanda, ta bada belin Alhassan Ado Doguwa

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke jihar Kano ta ƙalubalanci hukumar ‘yan sanda saboda kai Doguwa kotun da bata da hurumin sauraron irin laifin da ake tuhumarsa da shi, sanna ta bayar da belin Alhassan Ado Duguwa.

Baba Jobo kakakin kotunan Kano ya ce daman hakan yana kan tsari. Amma ya ce za a ci gaba da sauraron shari’ar zargin kisan kai da ake yi masa.

Yan sandan na zargin sa da hannu a harbin wasu mutane da bindiga kwana ɗaya bayan kammala jefa ƙuri’a a mazaɓarsa ta Doguwa/Tudunwada.

Ana kuma tuhumar ɗan majalisar da laifin kisan wasu mutum uku tare da raunata wasu guda takwas a ƙaramar hukumar Doguwa a lokacin da ake karɓa tare da bayyana sakamakon zaɓen ɗan majalisar.


Comments

3 responses to “Kotu ta ƙalubalanci hukumar ‘yan sanda, ta bada belin Alhassan Ado Doguwa”

  1. […] kU KUMA KARANTA: Kotu ta ƙalubalanci hukumar ‘yan sanda, ta bada belin Alhassan Ado Doguwa […]

  2. […] KU KUMA KARANTA: Kotu ta ƙalubalanci hukumar ‘yan sanda, ta bada belin Alhassan Ado Doguwa […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *