Hukumar Lafiya ta Duniya ta ba da rahoton ɓullar cutar korona (COVID-19) guda 674,678 daga ranar 23 ga Janairu zuwa 25 ga Janairun 2023.
Bayanan da aka samu daga hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO akan COVID-19 sun nuna cewa mutane 3,584 ne suka mutu sakamakon kamuwa da cutar a lokacin da ake nazari.
Wannan shi ne kamar yadda ƙungiyar lafiya ta duniya ta lura cewa, rigakafin COVID-19 ya kasance yana da matukar muhimmanci wajen kariya daga mummunan cuta da mutuwa, yayin da ƙwayar cutar ke ci gaba da yaɗuwa, kuma tana ci gaba da canzawa.
KU KUMA KARANTA:Ansamu masu cutar Ƙyandar-Biri a jihar Borno
Darakta Janar na hukumar ta WHO, Dr. Tedros Ghebreyesus, ya bayyana damuwarsa kan ƙaruwar adadin masu kamuwa da cutar COVID-19 a ƙasashe da dama.
Ghebreyesus ya ce Kwamitin gaggawa kan COVID-19 zai gana a wannan makon, don tattauna.
Rahoton da Majalisar Ɗinkin Duniya ta fitar ya nuna cewa,mutum 396,821 COVID-19 da aka tabbatar sun kamu da cutar a ranar 23 ga Janairu, tare da mutuwar 2,142. A ranar 24 ga Janairu, aƙalla 98,748 da aka tabbatar sun kamu da cutar tare da mutuwar 729.
Yayin da aka samu rahoton ɓullar cutar guda 179,108 da kuma mutuwar mutane 713 a ranar 25 ga watan Janairu.
Ya zuwa 25 Janairun 2023, an sami mutum 664,873,023 da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19, gami da mutuwar mutum 6,724,248, kamar yadda hukumar ta WHO ta ruwaito.
A wani ci gaba mai alaka da wannan, ofishin WHO na Afirka a Brazzaville ya ce ‘yan Afirka na fitowa daga lokacin balaguro na sabuwar shekara ba tare da an samu ɓullar cutar ta COVID-19 a karon farko tun bayan barkewar cutar ba.
Duk da haka, ya ce raguwar sabbin lamuran da aka bayar na iya kasancewa wani ɓangare saboda ƙarancin gwajin COVID-19, amma abu mafi mahimmanci shi ne rashin lafiya mai tsanani, da kuma mace-mace, sun ragu sosai.
A Najeriya an sami ƙararraki ararraki a halin da ake ciki, Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya ta tabbatar da samun sabbin mutane 15 da suka kamu da COVID-19 a cikin kasar cikin mako guda. An sami sabbin kararraki 15 daga 14 ga Janairu zuwa 20, 2023.
Rahotanni sun nuna cewa an samu rahoton ɓullar cutar daga jihohi huɗu – Filato (8), Kano (3), Legas (3), da Kaduna (1). Sabbin kararrakin guda 15 sun kawo adadin waɗanda aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a kasar zuwa 266,507, a cewar NCDC.
Hukumar ta ce, “Ya zuwa yanzu an tabbatar da kamuwa da cutar guda 266,507, an sallami mutane 259,864 sannan an samu mutuwar mutane 3,155 a jihohi 36 da kuma babban birnin tarayya.
Tun da farko, Gwamnatin Tarayya ta ce duk matafiya na duniya da suka isa Najeriya a yanzu ana bukatar su bayar da shaidar rigakafin a wuraren da ake shigowa da su biyo bayan ɓullar cutar COVID-19 a kasashen China, Japan, Amurka da sauran kasashe.
Gwamnatin Tarayya ta kuma ce fasinjojin da ba su da alluran rigakafin da suka taho daga wasu ƙasashe na iya zama dole a yi musu allurar a filin jirgin.
A halin da ake ciki, Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko ta ƙasa ta ce 65,679,094 na mutanen da suka cancanta da aka yi niyya don rigakafin COVID-19 a cikin ƙasar an yi musu cikakkiyar allurar rigakafin cutar yayin da 11,780,959 na mutanen da suka cancanta da aka yi niyya don rigakafin COVID-19 an yi musu wani ɓangare na allurar tun daga ranar 20 ga Janairu, 23.
A duniya baki ɗaya, an yi allurar rigakafin cutar guda 13,156,047,747 tun daga ranar 24 ga Janairun 2023.
[…] KU KUMA KARANTA: ‘Korona ta kashe sama da mutum dubu uku da ɗari biyar’ […]