Kimanin shaguna 50 ne gobara ta cinye a kasuwar Singa

Wata gobara ta tashi a kasuwar Singa ranar Lintinin, ta haifar da asara mai ɗinbin yawa.

Rahotanni sun ce wutar ta ƙona dukiya wadda har yanzu ba a iya tantancewa ba. Wannan dai shi ne karo na huɗu da ake samun gobara a baya-bayan nan a kasuwanni daban-daban na jihar Kano.

Bayanai na cewa gobarar ta auku ne da tsakar dare sanadiyar fashewar wani babban abin sanyaya ruwa a layin Savannah cikin babbar kasuwar ta Singa.

Wani mutum da lamarin ya auku a kan idonsa ya ce wutar ta yi mummunar ɓarna. “Duk wani da ke da rumfa a cikin inda gobarar ta faru bai iya fitar da komai ba,” in ji shi.

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tattabar da aukuwar gobarar. Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Saminu Yusuf Abdullahi ya ce wutar ta samo asali ne daga ɗakin sanyaya ruwa, sannan ya yaɗu zuwa wasu kantunan.

Ya ƙara da cewa rashin kyakkyawan tsarin ajiye kaya a kasuwar ya taimaka wajen iza wutar. Sai dai ya ce ba a samu rahoton rasa rai ko kuma na jikkatar wani ba a sanadiyyar gobarar.

Wannan dai ita ce gobara ta uku cikin kasa da wata biyu da ta auku a kasuwanni daban-daban a jihar Kano.

Kasuwar Singer dai babbar kasuwa ce da ake hada-hadar kayan masarufi daga sassan Najeriya har ma da ketare.

Alhaji Dan Azumi, wanda shi ne wakili a gidan Savannah, wurin da aka yi wanann gobara ya ce asarar da gobarar ta haddasa ta miliyoyin nairori ce.Ya ce “za a samu store kamar 50; akwai wanda yake da taliya, akwai kuma wanda yake da suga da kuma na kayan sinadarin miya.

“Ya ƙara da cewa akwai wanda ya sauke kayan sanadarin miya tirela biyar kwana ɗaya kafin ranar da gobarar ta tashi.Alhaji Dan Azumi ya ce a yanzu suna da kiyasin an yi asarar “biliyan biyu da wani abu.”


Comments

3 responses to “Kimanin shaguna 50 ne gobara ta cinye a kasuwar Singa”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Kimanin shaguna 50 ne gobara ta cinye a kasuwar Singa […]

  2. […] KU KUMA KARANTA: Kimanin shaguna 50 ne gobara ta cinye a kasuwar Singa […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *