Karamar Hukumar Dawakin Tofa Ta Biya Miliyan 10 A Matsayin Kudaden Karatu

0
409

Daga; JABIRU A HASSAN, Kano.

BISA yadda majalisar karamar hukumar Dawakin Tofa ta ke kokari wajen bunkasa Ilimi, shugaban karamar hukumar Alhaji Ado Tambai Kwa ya mika cekin kudade har na naira miliyan 10 ga makarantu daban-daban da daluban yankin ke karatu na sassan Kasar nan.

An gudanar da taron mika kudaden ne a ofishin shugaban kungiyar kasuwar kayan abinci ta duniya dake Dawanau bisa jagorancin wakilin karamar hukumar Dawakin Tofa a majalisar dokokin Jihar Kano Alhaji Saleh Ahmed Marke.

Cikin makarantun da aka biya kudaden, akwai makarantar koyon aikin jinya dake Kazaure watau “School of Health Technology Kazaure, sai makarantar Bichi Academy miliyan da makarantar koyon aikin jinya ta Halima Adamu.

Sauran makarantun sune Jami’ar Yusuf Maitama Sule da cibiyar kula da karatu ta Jihar Kano watau KERD da makarantar koyon aikin jinya ta Malumfashi Jihar Katsina, wanda akalla majalisar karamar hukumar Dawakin Tofa bisa jagorancin Alhaji Ado Tambai kwa ta dauki nauyin karatun dubban dalubai kuma ana basu kulawa ta musamman.

Mafi yawan mutanen da suka tattauna da wakilin mu sun bayyana cewa gwamnatin Alhaji Ado Tambai kwa ta zamo abar misali wajen bunkasa Ilimi da samar da yanayi mai kyau ga wanzuwar zaman lafiya a fadin yankin.

Leave a Reply