Kano da Bauchi sun lashe gasar Alƙur’ani ta ƙasa ta 2023

0
212

Malama Zainab Aliyu Muhammad daga jihar Kano ta zama gwarzuwar gasar Alƙur’ani ta ƙssa ta shekarar 2023 a ɓangaren mata a hadda da tafsiri.

A ɓangaren maza kuwa, Alaramma Ibrahim Muhammad Nasir daga Jihar Bauchi ne ya zama gwarzon shekara a musabaƙar karo na 38, wadda aka kammala a Jihar Yobe.

Mai Masaukin Baki, Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya karamma Malama Zainab Aliyu Muhammad daga Jihar Kano da kyautar mota ƙirar Honda Accord.

Alaramma Ibrahim Muhammad Nasir kuma gwamnan ya gwangwaje shi da kyautar mota ƙirar Honda Accord.

Sannan ya ba da kyautar bas mai ɗaukar mutum 18 ƙirar Toyota Hummer ga Kwamitin shiryar musabaƙa na ƙasa don ci gaba da ɗawainiyar gasar Alƙu’rani.

KU KUMA KARANTA: Yadda aka fara gasar Alƙur’ani ta ƙasa karo na 38 a Yobe

A ranar Asabar ɗin nan aka kammala gasar karatun Alƙur’anin ta ƙasa karo na 38 a Damaturu, fadar Jihar Yobe inda alarammomi daga sassan Najeriya suka nuna bajintarsu.

A lokacin rufe gasar, Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar, ya yaba wa matasan da suka shiga wannan gasar ta Karatun Alƙur’ani Mai Girma rukuni-rukuni, sannan ya yi musu fatan alheri.

Sarkin Musulmi, wanda shi ne ya jagoranci taron, ya nuna farin cikinsa bisa yadda aka gudanar da gasar a Yobe cikin kwanciyar hankali kuma a bisa tsari ba tare da an samu cikas ba.

Shi ma Shugaban Jami’ar Usmanu Dan Fodiyo da ke Sakkwato, Farfesa Lawan Sulaiman Bilbis ya yaba wa gwamna Mai Mala Buni bisa yadda ya ɗauki nauyin gasar da kuma yadda aka gudanar da ita cikin nasara.

Cibiyar Nazarin Addinin Musulunci na Jami’ar Danfodiyo ne dai ke shirya Gasar Alƙur’ani ta Ƙasa a Najeriya, kuma wanan shi ne karo na 38.

Mahalarta bikin rufe gasar ta Alƙur’ani sun haɗa da Gwamna Jihar Gombe, Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa, Inuwa Yahaya, Mataimakin Gwamna Jihar Borno, Mataimakin Gwamnan Jihar Taraba.

Sai masu girma sarakunan Jihar Yobe gaba ɗaya, ƙarƙashin Mai Martaba Sarkin Fika, sai Mai Martaba Shehun Dikwa da ya wakilci Mai girma Shehun Borno, sai Mai girma Sarkin Bauchi da sauran manya-manyan baƙi.

Leave a Reply