Kafinta ya kashe matarsa don ya mallake makarantar da ta gina

Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta kama wani kafinta mai shekaru 45 mai suna Segun Omotosho Ebenezer a ranar Lahadi, 20 ga watan Nuwamba, 2022 bisa laifin lakadawa matarsa ​​Omotosho Olubukola mai shekaru 42 ɗan karan duka har ta mutu.

A cewar mai magana da yawun ‘yan sanda a jihar Ogun SP Abimbola Oyeyemi, kamen wanda ake zargin ya biyo bayan ƙorafin da ‘yar uwar marigayiyar ta shigar a ofishin ‘yan sandan da ke Kemta a ranar 14 ga watan Nuwamba, 2022, inda ta bayyana cewa wanda ake zargin ya yi wa marigayiyar dukan tsiya tare da yi mata mummunan rauni.

Daga nan ne kuma ya garzaya da marigayiyar zuwa Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Idi-Aba Abeokuta, domin kula da ita, nan kuma ya bar ta a lokacin da take karɓar magani.

Mijin bai sani ba, marigayiyar ta aike da sakon murya ta WhatsApp ga ‘yan uwanta, inda ta sanar da su cewa mijin nata ya yi amfani da wani kwaɗon ƙarfe ya buga mata kai yayin da yake dukanta, kuma idan ta mutu to a sani cewa mijinta ne ya kashe ta.

Da aka kunna sautin muryar bayan yaji, asirinsa ya tono sai kafintan ya tsere.

Dangane da rahoton da kuma bayanan da ‘yan sanda suka samu, sai DPO mai kula da yankin Kemta, CSP Adeniyi Adekunle, ya umarci jami’an ya sanda su yi bincike, su kuma bi sahun mijin da ya kashe matarsa, a kuma kamo shi a duk inda yake.

Daga baya an gano shi ƙauyen Akinseku a Abeokuta inda ya ɓoye, kuma nan take aka kama shi.

Binciken farko ya nuna cewa, rigimar tasu ta samo asali ne saboda marigayiyar ta gina makaranta mai zaman kanta da sunanta da kuma sunan mijinta, wanda kafinta ne, wanda ya so ya karɓe ragamar kula da makarantar daga hannunta. wacce ke da takardar horon koyarwa ta NCE ta kuma nuna rashin amincewarta.

“Wannan shi ne dalilin da ya sa wanda ake zargin yayi ta dukan marigayiyar, har zuwa lokacin da ya kashe ta bayan yayi amfani da makullin karfe ya buga mata kai, wanda a ƙarshe ya yi sanadiyyar mutuwarta” inji Abimbola Oyeyemi.

A halin da ake ciki, kwamishinan ‘yan sandan jihar Ogun, CP Lanre Bankole, ya bayar da umarnin a miƙa wanda ake zargin zuwa sashin binciken manyyan Laifuka, na jihar domin ci gaba da bincike da kuma gurfanar da shi a gaban kuliya.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *