Kaduna 2023: Sani Sidi Ya Bayyana Niyarsa Na Tsayawa Takarar Gwamna A Jam’iyyar PDP

0
415

…Ya Gargadi Magoya Bayansa Da Yin Kamfen Na Batanci

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

TSOHON Shugaban Hukumar Bada Agajin Gaugawa ( NEMA), Honarabul Muhammad Sani Sidi, ya kai ziyarar neman goyon baya da bayyana ra’ayinsa bisa niyar tsayawa takarar Kujerar Gwamnan Jihar Kaduna a karkashin Jam’iyyar PDP domin darewa kan karagar Mulki na Gidan Gwamnatin Jihar ta Sir Kasim Ibrahim dake Kaduna.

Dan takarar Kujerar Gwamnan Jihar a ranar lahadi, ya fara da kai ziyara Ofishin Jam’iyyar a matakin karamar hukumar, Ofishin Shiyya ta Biyu, kana da zuwa Sakatariyar Ofishin Jam’iyyar ta PDP domin neman sa albarkarsu, kana da neman amincewarsu bisa kudirinsa na tsayawa takarar a karkashin Jam’iyyar.

Da yake jawabi a wajen taron, Alhaji Sani Sidi, ya bayyana cewa ya fara da kai ziyarar daga kasa ne saboda nuna sanin mahimmancin al’ummar dake wannan matakin, kana da bin Dokoki da ka’idodin da suka dace wanda yin hakan zai iya taimakawa wajen tabbatar masa da irin kaunar da al’ummar ke masa kamin ya runtuma izuwa sama domin bayyana niyarsa.

Tsohon Shugaban Hukumar (NEMA), ya kara da cewa ya kai wannan ziyarar ne bisa ra’ayinsa tare da magoya bayansa, tawagarsa da sauran al’umma wadanda suka aminta da cewa wannan tafiyar tasa ita ce tafiyar nasara, don haka ya je neman sa albarkar shugabannin da amincewarsu, kana da neman addu’arsu a gare shi.

Ya ce “wanda ya iya da wanda bai iya ba akwai banbanci don ita gaskiya, gaskiya ce kuma karya, karya ce, toh ni na fito wannan takara ne saboda kishi da bukatar ku na neman kwato wannan mulki daga hannun Jam’iyyar adawa ta APC izuwa PDP, don haka muke neman goyon bayan ku.”

“Mai girma Shugaban Jam’iyyarmu ta PDP mai albarka, muna so kasan cewa dukkanmu Ya’yan ka ne kuma muna son ka dauke mu a matsayin Ya’yan ka ba tare nuna wani banbanci ba ta hanyar bamu damar yin abubuwa yadda suka kamata, domin ta hanyar yin hakan ne zamu iya kawo ci gaban da ake bukata, kana da nasarar komawarmu a kan karagar Mulki.”

“Ina kira ga dukkanin magoya bayanmu musamman magoya bayana da adaina yin kamfen na batanci domin mutum daya ne zai yi Gwamna kuma wata kila ma bai ma riga ya fito ba, amma tunda Allah ne ke da mulki kuma Ya ce a nema a wajen shi, toh Allah Ya kaddara Sani Sidi ne Gwamnan, kuma Allah Yasa wannan tubalin da muka dora ya kaimu ga gidan Gwamnatin Sir Kasim Ibrahim na Jihar Kaduna.”

A nashi jawabin, Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Kaduna, Honarabul Hassan Hyet, ya bayyana Jindadinsu da gamsuwa bisa ga irin yadda Dan takarar ya zo ya gabatar da kansa, kana yake da tauhidin cewa mulki na Allah ne kuma shi ne mai badawa ga wanda yaso, amma suna masu masa fatan nasara a wannan tafiyar tasa ta neman kujerar Gwamnan Jihar ta Kaduna.

Acewarsa, ya godewa Allah da ya sanya dan takarar na daya daga cikin mutanen da suka tsaya takara a shekarar 2019 kuma ya ga irin yadda Jam’iyyar ta gudanar da harkokin ta a karkashin Jagorancin na shi, domin duk abinda aka yi duk a gabansu aka yi kuma tare dasu wanda hakan zai tabbatar musu da irin adalci da ake bukata.

Ya ce “idan Jam’iyya ba ta da yan takara, toh ba Jam’iyya ba ce, kuma idan Jam’iyya ba ta yi adalci a harkokin ta ba, toh babu shakka duk yan takara zasu watse, don haka muna kira ga yan takara da su yi kokarin halartar taron da za ayi a ranar talata domin sanin matakan da za a dauka yayin gudanar da harkokin siyasar da tsare-tsaren da ake bukata, don haka duk wanda ba zai samu zuwa ba, sai ya tura wakili amadadin shi.”

A karshe, Shugaban Jam’iyyar Hassan Hyet, ya shawarci Ya’yan Jam’iyyar da su yi kokarin sabonta katinsu na Jam’iyyar wanda da shi Jam’iyyar za tayi amfani, kuma nan bada jimawa za su soma bayar da katin a matakin Unguwanni ba a Jaha ko Tarayya ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here