Kada Mu Sakankance Domin Zaben 2023 Mai Zafi Ce Ba Kamar Na 2019 – Kawu Yakasai

0
386

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

TSOHON Shugaban karamar hukumar Soba dake Jihar Kaduna, Alhaji Kawu Yakasai, ya gargadi ‘ya’yan Jam’iyyar APC da kada su yi sakaci wajen nuna jajircewa da hadin kai domin zaben da za a gudanar a shekarar 2023 mai zafi ce ba kamar ta shekarar 2019 data gabata ba.

Da yake zantawa da manema labarai a dandalin murtala dake Kaduna jim kadan bayan kammala taron ganawa da wakilan Jam’iyyar APC da mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya yi a matsayin dan takarar shugaban kasa, ya bayyana cewa yanzu ba da bane don haka kowa dole ya daura damara.

Honarabul Kawu Yakasai, ya kara da cewa a shekarar 2023, al’umma yan takara zasu zaba ba Jam’iyya ba domin Shugaban Kasa Muhammadu ba zai tsaya takara ba balle har ya daga hannu wani ko wani dan takara ya jingina da shi.

Acewarsa, da akwai yuwar Jam’iyyar APC za ta yi nasara a zabukan shekarar ta 2023 da za a gudanar, to amma hakan ba yana nufin kada ‘ya’yan Jam’iyyar su nuna rashin jajircewa da kokari wajen ganin sun samu nasarori a lokacin zaben bane, face su kara hazaka da nuna kishi ta hanyar neman mafita don tabbatar da nasarorinsu.

Ya ce “ina so na jawo hankalin yan Jam’iyya cewa shekarar 2019, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne ke takara, kuma daidai gwargwado Allah Ya bashi farin jini amma yanzu ba zai sake tsaya ba, balle wani ya jingina da shi don haka dole yan takara su tashi tsaye su nemi Jama’a kada su Sakankance.”

“Kuma ina so na jawo hankalin yan takara, duk wanda Allah Yasa ya ci zaben fidda gwani ya dauka ya ci zaben duka gari, don haka su yi kokarin janyo sauran abokan takararsu wajen hada kai dukda kasancewa Jam’iyyar ta mu ta yi karfi, amma hakan ba yana nufin a koma a Sakankance bane.”

“Sannan ina ba yan takarar da idan aka yi zaben fidda gwani ba su yi nasara ba, da su rungumi kaddara su bi sauran yan Uwansu domin ayi Kamfen tare domin samun nasarar Jam’iyyar a zaben duka gari saboda hakan ne kadai zai ba da damar samun nasarorin da ake bukata.”

Da yake tsokaci game da ziyarar da Dan takarar Kujerar shugaban kasar ke nema, Tsohon Shugaban karamar hukumar Soba, ya bayyana cewa alamu sun nuna cewa zai yi adalci domin zai bar kofarsa a bude Shugabannin Jam’iyyar ba tare da takurawa ba, wanda hakan yasa a zuwansa yanzu sai da ya gaisa da duka yan takarar kuma suka dauki hoto.

Leave a Reply