Jirgin sama mai sauƙar ungulu ya faɗo a Legas

Wani jirgin sama mai sauƙar ungulu ya yi hatsari a yankin Ikeja da ke Jihar Legas a kudancin Najeriya.

Wani jami’in hukumar ba da agajin gaggawa ta Legas ya ce jirgin ya kama da wuta jim kaɗan bayan rikitowarsa da tsakar ranar Talata a kusa da filin jirgin sama na Murtala Muhammad.

KALLI CIKAKKEN BIDIYON ANAN:

Hukumar agajin gaggawa ta Najeriya, ‘National Emergency Management Agency’ (NEMA), ta ce mutum huɗu ne ke cikin jirgin kuma an ceto su da ransu.
Jami’in NEMA mai kula da sashen kudu maso yamma, Ibrahim Farinloye, ya ce ba su kai ga gano mamallakin jirgin ba ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.

Lamarin ya faru ne shekara uku bayan wani jirgin Helikwafta mallakar kamfanin Quorom Aviation ya faɗo a yankin Opebi na Legas ɗin a watan Agustan 2020.


Comments

2 responses to “Jirgin sama mai sauƙar ungulu ya faɗo a Legas”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Jirgin sama mai sauƙar ungulu ya faɗo a Legas […]

  2. […] KU KUMA KARANTA: Jirgin sama mai sauƙar ungulu ya faɗo a Legas […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *