Ministan sufuri na Najeriya, Sanata Hadi Sirika ya bayyana cewa jirgin saman kamfanin ‘Nigerian Air’ zai isa ƙasar ranar Juma’a a wani lamari da zai zama babban ci gaba ga shirye-shiryen soma tafiyar da harkokin kamfanin.
A hirar da ya yi da gidan Talabijin na Channels, ministan ya ce jirgin zai isa ƙasar ne cikin kwana biyu.
Ya yi alƙawarin cewa za a ƙaddamar da jirgin mai kalolin tutar Najeriya domin cika duka alƙawuran da gwamnatinsu ta yi a ɓangaren sufuri.
KU KUMA KARANTA: Ayi hattara da ‘hukumar EFCC na bogi’ – EFCC
Sai dai ya ce abin da ya rage kaɗai shi ne samar unguwanni kusa da filin jirgin sama wanda zuwa yanzu an kai kashi 60 cikin 100 na aikin.
A cewarsa, an kammala iza tubalin ginin kuma suna neman gwamnati mai zuwa ta ƙarasa aikin samar da unguwannin ta yadda zai sauƙaƙa wa mutane hawa jirgin.
Sirika yace a cikin watan Maris, yayin wani taron masu ruwa da tsaki a ɓangaren sufuri, ya ce kamfanin Nigerian Air zai soma aiki gadan-gadan kafin ƙarshen gwamnatin Muhammadu Buhari.
Da yake amsa tambaya kan takamaimen lokacin da Nigerian Air zai soma aiki, ministan ya ce “kafin ƙarshen wannan gwamnati, kafin 29 ga watan Mayu.”
Ya ƙara da cewa gwamnatin tarayya za ta bar ɓangaren sufuri cikin yanayi mai kyau fiye da yadda ta tarar da shi kasancewar an cimma fiye da kashi 90 cikin 100 na taswirar da aka tsara cimma a ɓangaren.
[…] KU KUMA KARANTA: Jirgin kamfanin ‘Nigerian Air’ zai iso Abuja ranar juma’a – Ministan sufuri […]