Jihohi sun fara tilasta yin gwajin shan ƙwaya a kan ma’aikata – NDLEA

0
12
Jihohi sun fara tilasta yin gwajin shan ƙwaya a kan ma’aikata - NDLEA

Jihohi sun fara tilasta yin gwajin shan ƙwaya a kan ma’aikata – NDLEA

Mai magana da yawun hukumar Femi Babafemi ya bayyana cewar wasu gwamnonin jihohin kasar sun rungumi fafutukar da ndlea keyi ta tilasta gwajin amfani da miyagun kwayoyi akan masu nadaddu da ma’aikata.

KU KUMA KARANTA:NDLEA a Legas ta kama hodar ibilis ta fiye da naira biliyan 4

Babafemi ya bayyana hakan ne a shirin tashar talabijin ta Channels na sassafe mai suna “Morning Brief” na yau Litinin.

A cewar babafemi, wasu daga cikin wadanda hukumar karkashin jagorancin Buba Marwa ta kama tare da gurfanarwa sun taba rike mukamai ya’alla a matakan kananan hukumomi. Zancen nan da muke a halin yanzu, akwai manyan mutane da dama dake fuskantar tuhuma a gaban kuliya a halin da aka ciki”.

Kakakin hukumar ta NDLEA ya kara da cewar bayan ga kasancewar hakan manufa ga mukaman siyasa, ma’aikata da manyan makarantu suma sun rungumi gwajin shan kwaya a matsayin wani bangare na aikin tantancewa gabanin daukar sabbin dalibai ko ma’aikata.

Leave a Reply