Jihar Kebbi za ta raba man fetur kyauta ga manoma

0
135

Gwamnatin Kebbi ta ɓullo da shiri na musamman domin raba man fetur kyauta ga manoman rani da nufin sauƙaƙa musu yin wahalar noma a jihar.

Kwamishinan Noma na jihar, Shehu Mu’azu ya ce gwamnatin ta samar da haujin noma, inda aka farfaɗo da aikin noma domin jihar ta cigaba da riƙe kambunta a ɓangaren noman shinkafa a Najeriya.

Saboda haka ne ta gina ƙaramin wurin noma na zamani a ƙananan hukumomin Argungu da Fakai a garin Mahuta.

Wannnan a cewarsa, ƙari ne a kan tallafin noman rani da manoman shinkafa 30,000 da masu noma masara 7,500 da kuma masu noman rogo 2,000 suka samu daga gwamnatin.

KU KUMA KARANTA: An ceto manoma 16 daga hannun masu garkuwa da mutane a Neja

Ya ƙara da cewa gwamnatin jiha ta biya kasonta na naira miliyan 350 a cikin shirin RAAMP, wanda zai samar da hanyoyin mota masu tsawon kilo mita 240 domin manoma su samu saukin sufuri, gwamnati ta sanya miliyan 350 a shirin.

Shehu Mu’azu ya sanar da hakan a taron manema labarai na sati-sati da ma’aikatar yada labarai ta shirya.

Leave a Reply