Jihar Kano Ta Ciri Tuta Wajen Bunkasa Ilimi – inji Dokta Kabir Bello

0
408

JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

SHUGABAN kwalejin fasaha ta Jihar Kano watau “Kano state polytechnic”, Dokta Kabir Ballo Dungurawa yace ko shakka babu gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje ta cancanci yabo dangane da kokarin da ta ke yi wajen bunkasa ilimi a matakai daban-daban.

Ya yi wannan tsokaci ne a jawabin da ya gabatar ranar Talatar da ta gabata yayin bikin aza harsashin ginin wani katafaren dakin daukar karatu na zamani wanda zai dauki dalubai 160 da cibiyar kwararru kan aikin banki da hadahadar kudade watau “Chartered Institute Of Banking Of Nigeria” (CIBN) zata gina sashen samun kwarewa kan sha’anin gudanarwa ta ” School Of Management Studies “.

Dokta Dungurawa ya kara da cewa, babu shakka suna masu matukar alfahari da irin goyon baya da kuma kulawa cikakkiya da Gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje ke baiwa fannin ilimi a fadin Jihar Kano duk da irin kalubalen da ake ciki na yanayin tattalin arziki da kuma gudanar da harkar ta ilimi, don haka wajibi ne su jinninawa maigirma Gwamna da Gwamnatin sa saboda wannan kokari da suke yi”.

Dangane da yadda wannan cibiya ta CIBN take aiwatar da aiyukanta kuwa, Dokta Kabir Bello Dungurawa ya jaddada farin cikin sa saboda samar da babban zauren daukar darussa irin na zamani da ta fara ginawa a makarantar sa tare da bayyana cewa da yardar Allah, za suyi amfani da wannan guri domin bunkasa koyo da bincike kan dukkanin abubuwan da suka shafi ilimin aikin banki.

Dokta Dungurawa, ya yi amfani da wannan dama inda ya godewa maimartaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da kwamishiniyar ma’aikatar ilimi mai zurfi Hajiya Mariya Mahmoud Bunkure da shugabamnin jami’oi da kwalejojin ilimi da kuma dukkanin masu ruwa da tsaki kan harka ilimi saboda halartar wannan biki da suka yi duk da irin harkokin aiki take gaban su.

Wakilin mu ya sami zantawa da shugaban kungiyar Dalibai masu karatu a fannin aikin banki watau Kwamared Nasiru Isah Musa,, inda ya shaida cewa Gwamnatin Ganduje ta cancanci yabo da godiya saboda kyautatawa fannin ilimi da ta ke yi Batare da nuna kasala ba, sannna ya bayyana shugaban kwalejin fasaha ta Jihar Kano Dokta Kabir Bello Dungurawa a matsayin shugaba wanda ya kawo ci gaba ingantacciya a makarantun dake karkashin ikon sa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here