Jami’ar Jihar Yobe ta yi bikin zuwan sabbin ɗalibai 2,740

Mataimakin Shugaban Jami’ar Jihar Yobe dake Damaturu, Farfesa Mala Mohammed Daura, ya bayyana cewa Jami’ar ta kai wani mataki na ɓullo da shirin koyon aikin jinya a Jami’ar, wato ‘B.Sc Nursing’ a Kwalejin Kimiyyar Kiwon Lafiyar.

Mataimakin shugaban jami’ar ya bayyana hakan ne a yau Laraba 19 ga watan Afrilu 2023 a wajen bikin maraba da zuwan sabbin ɗaliban jami’ar karo na 14.

Farfesa Daura ya kuma bayyana cewa Jami’ar na duba yiwuwar ɓullo da wasu shirye-shirye na ilimi a Kwalejin Kimiyyar Likita kamar Dentistry, Medical Laboratory Science da Radiography.

KU KUMA KARANTA: An yi kira ga hukumar Lantarki ta YEDC ta inganta yadda take ba da wuta a Yobe

Ya ce Jami’ar ya zuwa yanzu tana da ɓangaren Kwalejin Kimiyyar Kiwon Lafiyar Jama’a, rassa biyar, sassan ilimi 31 da ke gudanar da shirye-shiryen ilimi 48, da cibiyoyi na musamman guda 6.

Mataimakin shugaban jami’ar ya ƙara da cewa sabon ɓangaren noma da aka kafa tare da sassa huɗu na ilimi a yanzu haka ta fara karatu da ɗalibai 149 a matakin farko.

Ya ce jami’ar na samun ci gaba cikin sauri ta fuskar shirye-shiryen ilimi da kuma shigar da ɗalibai, inda ya jaddada cewa jimillar ɗaliban sun kai 11,022 kuma sun haɗa da sabbin ɗalibai 2,740 da kuma ɗalibai 8,282 da suka dawo daga matakin farko.

Farfesa Daura ya ci gaba da bayyana cewa ɗaliban da suka samu gurbin karatu na shekarar 2022/2023 su ne waɗanda suka nemi gurbin shiga ta hanyar UTME da DE a lokacin gudanar da jarabawar JAMB na 2021 da 2022.

Ya kuma buƙaci sabbin ɗaliban makarantar da su riƙa tunawa da irin rantsuwar da suka sanyawa hannu wajen gudanar da ayyukansu a ciki da wajen Jami’ar.

Mataimakin shugaban jami’ar ya kuma shawarci ɗaliban da su guji duk wata munanan ɗabi’u kuma su fuskanci karatunsu, su shiga ayyukan karatu tare da zama jakadu nagari na wannan Jami’a.

Daga nan sai Farfesa Daura ya ja hankalin iyaye da su yaba da ƙoƙarin gwamnatin jihar Yobe da gwamnatin tarayya wajen samar da ababen more rayuwa na koyo da koyarwa.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *