Iyaye sun gano ‘yarsu ta rasu, har bayan wata tara mijin be sanar dasu ba

0
326

Iyayen wata mata sun gano cewa mijin ‘yarsu ya ɓoye musu batun mutuwar ta har na tsawon wata tara, inda da suka gano, sai ya bayyana musu cewa ya manta ne shi yasa bai sanar dasu ba.

Wani mutum mai suna Abubakar ya wallafa a shafin shi na tuwita mai suna Fadhlu_S labarin yadda wani miji ya binne matar shi da ta mutual, wata tara da suka gabata ba tare da sanar da iyayen ta ba.

Yadda ‘yan tiwitter keta tofa albarkacin bakinsu

Kamar yadda Fadhlu ya bayyana, iyayen matar basu sani ba har sai Asabar ɗin nan, 22 ga Oktoba 2022, bayan da wata mata taga ƙabarin nata, inda daga nan ne ta tuntuɓe iyayen don sanar dasu. Neptune Hausa ta gano cewa Iyayen na zaune ne a Cameroon, ita kuma yarinyar tasu na aure a Amurka.

Jin hakan keda wuya sai iyayen matar suka kira mijin sannan suka tambaye shi ko menene gaskiyar zancen. Kada bakin shi keda wuya, sai ya ce musu shi ya manta ne bai sanar dasu cewa ta mutu ba.

Sai dai kuma Fadhlu ya caccaki mijin, inda ya kira shi da azzalumi sabili da ya bar wayar matar a kunne, kira nata shigowa ba tare da ya na ɗaga wa ba, har zuwa sanda wata taga ƙabarin sannan ta sanar da iyayen matar.

“Eh ya mance, amma kuma sai ya bar wayar tata a buɗe ana ta kira ba tare da ana amsawa ba. Sai da wata mata taga ƙabarin jiya a maƙabarta sannan sai ta kira iyayen ta, wanda a sannan ne suka sani. Sun tuntuɓi mijin inda anan ne yake bayyana musu cewa eh lallai ta mutu wata tara da suka gabata, amma ya mance bai sanar dasu ba.

“Wasu mutanen azzalumai ne wallahi, matar ka ta mutu watanni 9 da suka wuce, amma kuma ka mance ka kira iyayen ta. Ka cigaba da yima wayarta caji amma ka ƙi amsa kiraye-kirayen da ake mata. Ina! Akwai hisabi.” Fadhlu ya rubuta.

Masu amfani da shafin tiwitter sun harzuƙa, inda wasu ke cewa ‘shine ma ya kashe ta, idan ba haka ba, menene dalilin ɓoyewa iyayen ta mutuwarsa?”. Wasu kuma sukace, ɗan ƙungiyar asiri ne, ya sadaukar da matar ne kawai”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here