Islamiyoyi sama da ɗari biyar ne suka fito zagayen Maulidi a Potiskum

1
417

Daga Ibraheem El-Tafseer

Kamar yadda aka saba a kowace shekara, a Asabar ɗin farko na watan Rabiul Awwal (watan haihuwar Annabi Muhammad SAW) ɗaruruwan al’ummar musulmi ne masoya Manzon Allah (SAW) haɗe da dukkan Islamiyoyi na cikin garin Potiskum, suke fitowa zagayen Maulidi, don nuna murna da zagayowar watan da aka haifi Annabi Muhammad (SAW).

Dubban al’ummar musulmin, suna taru wa ne a ƙofar fadar mai martaba Sarkin Fika, daga nan sai a shiga sahu ana zagaya manyan titunan cikin gari, ana salati da yabo ga Manzon Allah Muhammad (SAW). Ana fito wa ne, maza da mata, yara da manya, kowa cikin ado, farin ciki da shauƙi.

KU KUMA KARANTA: Meye ra’ayinka kan mauludi? Tattaunawarmu da wani a kan Mauludi, Daga Yusuf Alhaji Lawan

Malaman Darikar Tijjaniyya, Qadiriyya da Shi’a sune kan gaba wajen gudanar da wannan zagayen Maulidi. Shaikh Mukhtari Waliy Ibn Shaikh Kabir Potiskum, shi ne shugaban kwamitin gudanar da zagayen maulidin a garin Potiskum, ya bayyana cewa “muna fito wa zagayen maulidi ne, don nuna soyayya ga Annabi Muhammad (SAW).

To daga yau kuma mun buɗe ƙofar tarurrukan Maulidi a lunguna da saƙuna, don bayyana haƙiƙanin kyawawan halayen Manzon Allah da ɗabi’unsa ababen koyi”

Zagayen Maulidin an shafe awa huɗu ana gudanar da shi. A ƙarshe, aka yi addu’a aka tashi.

1 COMMENT

Leave a Reply