Iraƙi ta haramta wa wasu bankunan ƙasar 8 hada-hada da Dalar Amurka

0
209

Daga Maryam Umar Abdullahi

Ƙasar Iraƙi ta haramtawa bankunan ƙasar 8 yin hada-hada da dalar Amurka, a matsayin matakin rage damfara, hallata kuɗaɗen haram da sauran wasu hanyoyi da ake amfani da dalar Amurka don yin abubuwan da suka saba doka, wannan na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan ziyarar da wani babban jami’in baitulmalin Amurka ya kai.

An haramtawa bankunan damar samun dala a sauƙaƙe a duk rana daga babban bankin Iraƙi, babbar hanyar samun kuɗaɗen ƙasar waje a ƙasar da ta dogara ga shigo da kayayyaki daga waje, wadda kuma Amurka ke sa wa ido a ƙoƙarin ta na magance safarar kuɗaɗe zuwa maƙwabciyar ƙasar Iran.

Ƙasar Iraƙi, da ke zaman abokiyar hulɗa ga Amurka da Iran, wadda ke da kuɗi fiye da dalar Amurka biliyan 100 ajiye a Amurka, ta dogara sosai ga taimakon Amurka domin tabbatar da ganin ba a toshe mata kuɗaɗe da hanyar samun kuɗin shiga daga saida man ta ba.

Wata takardar babban bankin ƙasar da wani jami’i a bankin ya tabbatar da sahihancinta ce ta bayyana sunayen bankunan da aka haramtawa amfani da dalar.

KU KUMA KARANTA:INEC ta dakatar da wani jami’inta don gudanar da bincike kan ɓacewar takardun kaɗa ƙuri’a

Shugaban ƙungiyar bankuna masu zaman kansu na Iraƙi, wanda ke wakiltar bankunan da abin ya shafa, da bankunan Ashur da Hammurabi, nan take basu amsa buƙatar su maida martani ba.

Wani mai magana da yawun baitulmalin ya ce: “Mun yaba da yadda babban bankin Iraƙi ke ci gaba da ɗaukar matakai don kare tsarin hada-hadar kuɗi na ƙasar daga masu muzanta shi.”

A watan Yulin shekarar 2023, Iraƙi ta haramta wa bankuna 14 gudanar da hada-hadar dala a matsayin wani ɓangare na yaƙi da safarar dala zuwa Iran ta hanyar bankunan Iraƙi. An ɗauki matakin ne bayan wata buƙata daga Amurka, a cewar jami’an Iraƙi da na Amurka.

Leave a Reply