Iran za ta dasa na’urorin ɗaukan hoto don kama matan da ba sa saka hijabi

Adadin matan da ke take dokar saka Hijabi a ƙasar Iran na ci gaba da ƙaruwa a ‘yan kwanakin nan, tun bayan jerin zanga-zanga da aka yi a lokacin mutuwar wata Baƙurdiya ‘yar shekara 22 mai suna Mahsi Amini, wacce aka zarga da keta dokar.

‘Yan sanda a Iran sun ce za su fara amfani da fasahar zamani a wuraren da jama’a ke kai-komo don ganowa tare da hukunta matan da ke karya dokar saka Hijabi a ƙasar.

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin tarayya ta amince da sanya hijabi a makarantun sakandare

Wata sanarwa da hukumomin Iran suka fitar a ranar Asabar ta ce, “za a fara amfani da na’urorin ɗaukan hoto ko kyamara a wuraren da jama’a suke, domin gano masu bijirewa dokar.”

Sanarwar ta ƙara da cewa, “za a riƙa aika wa masu take dokar shaida da kuma saƙo na gargaɗi kan yiwuwar a ɗaukar matakin shari’a akansu idan suka sake take dokar.”

Amini ta rasu ne a hannun ‘yan sanda a lokacin da ake tsare da ita bisa tuhumar karya dokar saka Hijabi.


Comments

One response to “Iran za ta dasa na’urorin ɗaukan hoto don kama matan da ba sa saka hijabi”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Iran za ta dasa na’urorin ɗaukan hoto don kama matan da ba sa saka hijabi […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *