Iran ta ce a shirye take ta taimakawa jamhuriyar Nijar, don shawo kan takunkuman da aka ƙaƙaba mata

0
193

Daga Maryam Umar Abdullahi

Iran ta faɗa a jiya Laraba cewa, a shirye take ta taimaka wa Jamhuriyar Nijar da aka yi juyin mulki, don shawo kan takunkumin da ƙasashen duniya suka ƙaƙaba mata, a daidai lokacin da Iran ke ƙoƙarin rage maida ita saniyar ware da aka yi, ta hanyar ƙarfafa alaƙa da ƙasashen Afirka.

Mataimakin shugaban ƙasar Iran, Mohammad Mokhber, ya ce ƙasarsa ta yi Allah wadai da takunkumin na rashin Imani, a wata ganawa da Firai Ministan Nijar Ali Mahaman Lamine Zeine.

Ya ƙara da cewa “Babu shakka zamu bayyanawa abokanmu daga Nijar abinda mu ka koya a wannan”

Tun bayan nasarar juyin Musulunci a shekarar 1979 aka ƙaƙaba wa Iran takunkumi mai tsanani daga ƙasashen duniya, amma ta samu hanyoyin kaucewa wasu daga cikinsu.

An ƙaƙaba wa Iran takunkuman ƙasa da ƙasa masu tsauri tun bayan juyin-juya hali na Musulunci a shekara ta 1979, amma ta samu hanyoyi fidda kanta daga waɗansu.

KU KUMA KARANTA:Sama da mutane 70 ne suka mutu, sakamakon rugujewar mahaƙar Zinari a ƙasar Mali

Har ila yau Iran na fuskantar matsin takunkuman da Amurka ta ƙaƙaba mata tun bayan ficewar da Washington ta yi a shekarar 2018 daga wata muhimmiyar yarjejeniyar nukiliya da ta bai wa Iran sassaucin takunkumi domin daƙile ayyukanta na nukiliya.

Ƙasar Nijar na fuskantar tsauraran takunkumin tattalin arziƙi da na kuɗi daga ƙungiyar ƙasashen yammacin Afirka bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Yulin 2023 wanda ya hamɓarar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Mohamed Bazoum.

A cikin taron, Mokhber ya yaba da “nasarar” da ƙasar da Faransa ta yi wa mulkin mallaka ta yi, na “kafa gwamnati mai cin gashin kanta” a lokacin wannan juyin mulkin.

Ƙasashen biyu sun tattaɓa hannu kan yarjeniyoyi da dama a fannoni daban-daban da suka haɗa da makamashi, kiwon lafiya da kuɗi.

A watannin baya-bayan nan Iran ta tabbatar da goyon bayanta ga shugabannin da suka ƙwace mulki ta hanyar juyin mulki a Mali, Burkina Faso da Nijar.

Shugaban ƙasar Iran Ebrahim Raisi a watan Satumba ya yaba da “jajircewar waɗannan ƙasashen na Afirka” waɗanda ke fuskantar “manufofin Turai da mulkin mallaka.”

Iran, kamar Rasha da Turkiyya, a shirye take ta ƙarfafa tasirinta a nahiyar Afirka, inda take ƙarfafa alaƙa a ƙoƙarin ta na rage wariyar launin fata da maida ta saniyar ware da aka yi, da kuma kawar da tasirin takunkumin.

Leave a Reply