IMC Kaduna, Ta Gudanar Da Taron Bita Domin Samar Da Mafita Kan Matsalar Cin Hanci Da Rashawa

0
334

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

CIBIYAR Sasanci tsakanin Addinai dake Kaduna, wato Interfaith Mediation Centre, Kaduna (IMC), ta gudanar da wani taron Bita domin jin ra’ayoyin al’umma bisa samar da mafita a kan matsalar cin hanci da Rashawa da ya addabi al’umma musamman a yankin karkara ta kasar Najeriya.

Taron wanda ya gudana a ranar Asabar tare da hadin gwiwar Cibiyar nazarin damokuradiyya na Gidan Mambayya ta Aminu Kano dake Kano da Gidauniyar MacArthur, kana Gidauniyar Catherine MacArthur ta dauki nauyinv, an gudanar da shi ne a garin Kaduna domin bayyana irin kalube da nasarorin da aka samu ta fannin yaki da cin hanci da rashawa a matakin karkara.

Da yake jawabi a wajen taron, Daraktan ayyuka na Cibiyar Mambayya, Rabaren Dakta James Movel Wuye, ya bayyana cewa makasudin gudanar da taron shi ne domin tantance amfani da rashin amfanin shiga karkara da aka yi domin a fitar da mutanen da suke gaba da cin hanci da rashawa, kana a kafa Kungiyoyi na matasa a sassa daban-daban wanda zasu taimaka wajen ganin an magance matsalar a matakin karkara.

Ya kara da cewa hakan shi ne ya basu damar hada wannan taron tare da manyansu wadanda suka hada da Kansiloli, Shugabannin kananan hukumomi, Sarakuna, Malaman Addinai da matasa maza da mata a bangarori daban-daban dake wasu kananan hukumomi a fadin Jihar Kaduna domin kunyata mutanen da ke borewa yaki da aikin cin hancin da rashawan.

Ya ce “manufar wannan taron shi ne don ganin an yi yaki da cin hanci da rashawa domin a daina shi akowani mataki koda ko na yin lattin zuwa aiki ne, kin biyan kudin kasa, biyan hakkunan kudin wuta da sauran abubuwa ne, kuma ana cin nasara a kan wannan aiki da muka dauko wanda kadan daga cikin bayanan da ake gabatarwa na tabbatar da hakan.”

Hakazalika, da yake bayani Sarkin Gabas na Tudun Wada Kaduna, Alhaji Gombo Ibrahim, ya bayyana cewa su Kansu Shugabannin al’umma na da irin nasu laifin domin duk abin da za a ba mutum da sunan na Goro ne, wani mataki ne na ba da cin hanci saboda haka ya kamata su kiyaye domin da mai bayarwa da mai karba duk masu laifi ne a wajen Ubangiji.

Acewarsa, cin hanci da rashawa wani babban al’amari ne na gama gari da ko’ina a cikin al’umma ana samun shi domin ko a cikin gidajen al’umma ana samun shi wanda ya zama wajibi ayi yaki da shi, kuma yana da yakinin su wadanda suke gudanar da ayyukan kan shirya taron, su sun hango abin da suka gani domin tabbatar da an samu nasarar yin yaki da shi a tsakanin al’umma.

Shi ma da yake tofa albarkacin bakinsa, Farfesa Moses T Aluaigba na sashen bincike a Gidan Cibiyar Mambayya, ya bayyana cewa wannan matakin da suka dauka na ganin cewa an dakile yawaitar yaduwar cin hanci da rashawa a kasar musamman a yankin karkara, wani aiki ne wanda zai dan dauki lokaci, to amma suna iya bakin kokarinsu wajen ganin an cimma nasara a aikin nasu.

Ya kara da cewa, duk da kasancewar yaki da cin hanci da rashawa ba karamin al’amari bane, to amma sannu a hankali za su cimma nasarar da ake bukata ta hanyar canza ra’ayoyi da dabi’un mutane, domin ko yanzu bayanan da suke samu daga bakin mutanen da suke gudanar da ayyukan a karkara karkashin Jagorancin Cibiyar Sasanci tsakanin Addinai (IMC) na tabbatar da ana samun nasara da ake bukata kadan-kadan.

Taron Bitar ya samu halartar al’umma daban-daban ciki har da wasu Kansiloli da wasu wakilan Shugabannin kananan hukumomin Chikun, Kaduna ta Arewa da kidu, Kungiyoyin matasa maza da mata, Dalibai da Malaman Makaranta, da yan Jaridun da suke kokarin yada manufar gudanar da ayyukan a cikin al’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here