Hukumomin tsaron Najeriya sun yi nasara kan ‘yan IPOB

1
321

Hukumomin tsaro a Najeriya sun ce sun samu nasarar kama manyan kwamandojin ƙungiyar da ke fafutikar kafa ƙasar Biafra ta IPOB, da raunata ƴan kungiyar da dama a jihar a Ebonyi da ke kudancin ƙasar.

Wata sanarwa da kakakin ‘yan sandan jihar SP Chris Anyanwu ya fitar ta ce sun kama ƴan kungiyar ne a wani samame da suka kai, a sansanin ‘yan IPOB ɗin uku da ke jihar.

Rundunar ‘yan sandan ta ƙara da cewa sun kai samamen ne da hadin gwiwa da ‘yan sandan farin kaya, kuma bayanan da ‘yan kungiyar biyu da aka kama ne suka ba su bayanan.

Sai dai ‘yan IPOB ɗin ne suka fara budewa jami’an tsaron wuta, kuma sun yi nasarar cafke wani ɗan ƙungiyar da suka daɗe su na nema ruwa a jallo, kan zargi hannu da kai hari babban ofishin ‘yan sanda ke jihar, an kuma kashe wasu ya yin da sauran suka fada kogin Ofeke tare da tserewa. Sun kuma yi nasarar kwace makamai.

A ranar Litinin ne za a sake zama a kotun ɗaukaka ƙara, kan batun belin jagoran masu fafutukar kafa jamhuriyar Biafra Nnamdi Kanu wanda gwamnatin Najeriya ta buƙaci a dakatar da hukuncin da wata kotun ɗaukaka kara ta yi na buƙatar a saki Kanu.

1 COMMENT

Leave a Reply