Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa ta shirya taron ƙarawa juna sani ga ‘Yan Jarida da ma’aikatanta

0
174

A ranar Alhamis, hukumar ƙidayar jama’a a Najeriya (NPC) ta shirya taron ƙarawa juna sani ga Ma’aikatanta da ‘yan jarida, domin samun ƙwarewa da kuma yaɗa yadda aikin ƙidayar zai kasance.

Taron da hukumar ta NPC daga shiyyar jihar Katsina ta shiryashi na wuni ɗaya domin bita akan yadda aikin ƙidayar na zamani yake da yadda zai kasance. Inda masana suka karanta muƙaloli akan ƙidayar da tarihin ƙidayar da ire-iren ci gaban da aka samu akan ƙidayar tun daga shekarun fara ƙidayar a Najeriya.

Muƙaloli da aka gabatar da harshen turanci daga bakin Masana sun haɗa da: “Enumeration Area Demarcation for the 2023 Population and Housing.” wato ‘Ƙidaya don tantance yawan jama’a da gidaje na shekarar 2023’ Wanda Ibrahim Garba Daura ya gabatar.

KU KUMA KARANTA: Kimanin Yara Miliyan 13 Ne Ba Sa Zuwa Makaranta A Najeriya – UN

“Process and Methodology for the 2023 Population and Housing Census.” wato ‘Tsari da dabaru don ƙidayar yawan jama’a da gidaje na 2023’ tare da Saminu Sada Senior Cartographer.

“Technological Innovation in the 2023 Population and Housing Census.” wato ‘Ƙirƙirar fasaha a cikin ƙidayar yawan jama’a da gidaje na 2023’ tare da Ado Mamman, Senior Planing Officer.

“History of Population Censuses In Nigeria and Structure and Mandate of National Population Commission.” wato ‘Tarihin ƙidayar yawan jama’a a Najeriya da dsari da wa’adin hukumar yawan jama’a ta ƙasa’ tare da Yusuf Hussain, HOD Census Department.

sai “How to generate Media contents on the 2023 Population and Housing Census.” wato ‘Yadda ake tattara rahotanni da yaɗa ƙidayar yawan jama’a da gidaje na 2023’ Wanda Ayinde Razaq, HOD Public Affairs Department, ya gabatar.

Inda daga bisani aka gabatar da tambayoyi da amsoshi. Haka yake a kusan dukkanin jihohin Najeriya, don gudanar da aikin cikin fahimta da tsari.

Leave a Reply