Hukumar zakka da waƙafi ta raba kayayyakin jin ƙai ga marasa galihu a Zamfara

0
116

Daga Abdullahi Musa

A ‘yan makonnin da suka gabata ne Hukumar Zakka da Waƙafi ta jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin Sheikh Umar Ahmad Kanoma, ta ɓullo da wasu sabbin hanyoyi da tsare-tsaren taimaka wa wajen canza rayuwar al’umma da kyautata jin daɗi da kuma zamantakewarsu.

Hukumar ta ƙarfafa hanyoyin da aka san ta da su na jajircewa wajen yi wa al’umma hidima cikin tausayi da adalci, Hukumar ta samu gagarumin ci gaba a ayyukanta na rage raɗaɗin talauci da ƙarfafa wa marasa galihu a lokacin Azumin watan Ramadan da ya gabata.

Habib Balarabe Muhammad,
Sakataren zartaswa na hukumar zakka da waƙafi na jihar Zamfara

Bisa kulawar sakataren zartaswa, Habib Balarabe Muhammad, Hukumar ta samu gagarumar nasara wajen tallafa wa mabuƙata da marasa galihu.

Hukumar ta kai ɗaukin gaggawa ga mata masu fama da matsalar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da haifar masu da fata a zukatansu, ta hanyar shirya masu tarukan faɗakarwa da nufin kyautata rayuwarsu.

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Katsina za ta kafa hukumar Zakka – Raɗɗa

Baya ga samar wa mata da matasa marasa galihu hanyoyin dogaro da kai, Hukumar ta tallafa masu da mahimman kayayyakin koyon sana’a da haɓaka ƙwarewa a tsakaninsu. Wannan tsarin jin ƙai yana nuna sadaukarwar Hukumar don jin daɗin marasa galihu.

A cikin watan Ramadan, Hukumar ta ƙara ƙaimi, inda ta tallafa wa mutane sama da 40,000 a faɗin jihar Zamfara da kayan abinci da taimakon kuɗi.

Bugu da ƙari, Hukumar ta samar da gaɓoɓin roba kyauta ga mutanen da suka rasa gaɓoɓinsu sakamako hatsura ko ayyukan ‘yan ta’adda da taimaka wa mata masu matsalar cutar yoyon fitsari (VVF). Hakan ya jaddada himmar Hukumar wajen samun damar kiwon lafiya da nufin inganta rayuwar marasa galihu.

Ta hanyar haɗin gwiwa da ƙungiyoyi jin ƙai kamar; Bright Futures Serious da Organised Crime Prevention Project (SOC), Hukumar ta samar da tsare-tsare don rigakafi da kuma tsarin tallafi, tabbatar da samari masu aikata laifuka sun sami jagoranci na gari a rayuwarsu da nufin ƙarfafa su don kawar da aikata miyagun laifuka a tsakanin al’umma a jihar.

Bayan sallar Eid al-Fitr, Hukumar ta kasance mai himma, tare da yin alƙawarin shigar ɗaruruwan mutane a cikin shirye-shiryen gina rayuwarsu da dabarun haɓaka fasaha. Wannan tsarin sa ido yana nuna sadaukarwarsu ga ƙarfafawa ta dogon lokaci da nufin samar da mafita mai ɗorewa ga al’umma.

Nasarorin da Hukumar ke samu sun nuna muhimmancin samar da kyakkyawan tsari da irin tasirin da yake da shi. Tun daga yunƙurin agajin gaggawa zuwa shirye-shiryen ƙarfafa wa na dogon lokaci, kowane aiki yana ƙunshe da ƙa’idojin haɗin gwiwa da jin ƙai da ke cikin Zakka.

Hukumar ta yi alƙawarin kiyaye ƙa’idodin aiki, haɓaka haɗin gwiwa, da ɓullo da sabbin hanyoyi don magance talauci da kuma fuskantar ƙalubalen tattalin arziƙi yadda ya kamata.

Tare da jajircewa wajen yi wa al’umma hidima bisa tsarin addinin Musulunci, Hukumar Zakka da Waƙafi ta jihar Zamfara ta tsaya tsayin daka a matsayin wata fitilar da ke haskaka rayuwar marasa galihu da kuma samar masu da fata a rayuwa.

Leave a Reply