Hukumar ‘yansanda sun cafke mazan da suka yima yarinya fyade, da miƙata ƙungiyar asiri a Ogun

1
467
symbolic picture of violence at home

Labari daga Fatima MONJA, Abuja

Rundunan ‘yan sandan jihar Ogun ne suka yi caraf da wasu matasa da ake zargin ‘yan kungiyar Eiye Confraternity ne, an kama su bisa tilastawa wata yarinya shiga kungiyar ƙarfi da yaji bayan yi mata fyade.

Kakakin ‘yan sandan, DSP Abimbola Oyeyemi ya bayyana hakan a wata sanawar da ya fitar ranar Lahadi a Ota, da ke jihar Ogun, yace an kama wadanda ake zargin ne a ranar talatin ga watan yuni a yankin ajiwun na jihar.

Ya kuma bayyana cewa an kama su ne bisa rahoton da mahaifiyyar wacce aka ketawa haddi ta kai ofishin ‘yan sanda dake Ajuwon na jahar.

Da yake bayani, Oyeyemi ya bayyana sunan wanda ake zargin, Daniel Njoku wanda aka fi sani da (Agege), Adebayo Olamilekan, da kuma Damilare Ogundiran.

A cewar mahaifiyar wacce akayiwa fyade, ta aika diyar ta ‘yar sheraku 15 zuwa yankin akute Odo, sai shi Daniel Njoku yayi ikirarin cewa aurenta yayi.

Njoku shine ya dauketa ya kaita ga kungiyar sa a maɓoyar su, inda akayi ma yarinyar fyade da dukkan lalatan da suka mata. Kana suka mata barazan kashe ta in har ta bayyana ma kowa lamarin.

Bayan rahoton, jami’an yan sanda na Ajuwon, SP Andrew Akiseye, yayi bayani ga jami’an yan sandan da zasu bi bayan ‘yan kungiyar.

“Tawagar da tayi aiki da bayanan sirri ta gano maɓoyar ‘yan kungiyar da zasu shiga musamman mata.

A halin da ake ciki kwamishinan yan sanda Lanre Bankole ya bada umarnin mika wadanda ake zargi zuwa sashen yaƙi da ‘yan kungiyar asiri ta jihar.

1 COMMENT

Leave a Reply