Daga; Rabo Haladu.
Hukumar ta Kwastom Shiyar Arewa dake Kaduna ta gabatarwa da al’umma irin kayayakin da tayi nasarorin kamawa a cikin wannan wata na Afirilu 2022.
Wannan bayanai sun fitone a yayin zantawar Shugaban Hukumar Kwastom, Kwanturola Albashir Hamisu dake shiyar Arewa da manema labarai a ofishinsa a ranar 26 ga watan Afrilu a Kaduna.
Acewar Kwanturol Albashir Hamisu, a cikin kaya 96 da suka Kama wanda kudinsu yakai jimilar naira Miliyan N232,530,050.42 daga 23 ga watan Maris zuwa 25 ga watan Afrilu na 2022.
Ya ce kadan daga cikin kayan da suka Kama a hannun ‘yan fasa kwarin sun hada da buhunan shinkafar ‘Yar waje 1,314 wanda kudinta yakai N219,00 da magungunan asibiti marasa rijista katon 642 da taliya ‘yar waje da makaroni 30g sannan Kuma sun kama jarkokin man fetur Mai nauyin Lita 25.
Kwanturola Albashir Hamisu, ya ce sun kama buhunan wake wanda aka gawrayashi da shinkafa ‘Yar waje 15 Mai nauyin kg 100 tare da kama dilar gwanjo 94.
Acewar kwanturola Albashir Hamisu sun yi aiki da dokar data hana shigo da kayan ba bisa kaidaba Mai lamba C45 LFN ta 2004.
Kwanturola Hamisu ya godewa alumma da suke basu hadinkai da goyan bayan nasanar da su mahimman bayanai nasanar da su hanyoyin da za abi wajan kawar da fasa kwori.
Haka kuma ya godewa Hukumar kwastum saboda karin girman da aka yiwa Jami an nata.