Daga Shafa’atu DAUDA, Kano
Hukumar Hisbah a jihar Kano ta sha al’washin samar da sabbin dokokin da za su hukunta masu yin bara da ƙananan yara ko ‘yan jagora, kuma a kan titunan ƙwaryar birnin Kano.
Mataimakin Babban kwamadan hukumar ayyuka na musanman, malam Hussain Ahmad Cediyar kuda shi ne ya sanar da hakan a ya yin horan mabarata 39 waɗanda dakarun hukumar Hisbah su ka kama na aiwatar da laifin yin bara, ciki har da masu ɗauke da ƙananan yara a manyan titin Kano.
Malam Hussain Ahmad Cediyar Kuda ya ƙara da cewar Hisbah ba zatayi ƙasa a gwiwa ba, wajen samar da sabbin hanyoyin kawar da masu yin bara da dukkanin ma su yi musu jagora, a kan titunan ƙwaryar birnin Kano ko a shataletalen da sauran wuraren ba da hunnun motoci masu kai komo.
Tun da fari jami’in hukumar Hisbah mai kula da hana barace barace a kan titunan ƙwaryar birnin Kano, malam Abubakar Salihu yace sun sami nasarar kamo mabarata a kan titi maza da mata 39 ciki har da ‘yan jagora ya yin da su ke tsaka da yin bara a kan titunan ɗan Agundi da titin murtala Muhammad way da titin gidan murtala da titin zuwa gidan gwamna da danjar magwan.
Malam Abubakar salihu ya ci gaba da cewar sauran wuraren sun hadar da kofar famfo da kofar kabuga da shataletalen Tal’udu da titin gidan shatima duk a kwaryar birnin Kano.