Hukumar EFCC ta kori jami’anta 27 daga aiki

0
44
EFCC ta kori jami’anta 27 daga aiki

Hukumar EFCC ta kori jami’anta 27 daga aiki

Hukumar Yaƙi da Masu Karya Tattalin Arziƙi (EFCC) ta kori jami’anta guda 27 kan aikata laifukan almundahana.

Hukumar ta ce laifukan sun ci karo da dokokin aikinta, don haka ya tuɓe musu kaki.

Duk da ce ba ta bayyana sunaye da muƙaman jami’an da ta kora ba, amma ta bayyana cewa shugaban Hukumar, Ola Olukoyede ya riga ya sa hannu kan takarda korar.

Olukoyede ta hannun kakakin Hukumar EFCC, Dele Oyewale, ya ce an kori ma’aikatan da abin ya shafa ne bayan karɓar kwamitin bincike da ladabtrwar hukumar da ta binciki zarge-zargen da ake musu, kuma aka same su da laifi.

KU KUMA KARANTA: Shugaban EFCC ya umarci jami&;ansa su binciki gwamnonin da ke kan mulki

Ya ƙara da cewa Hukumar za ta binciki zargin almundahanar Dala dubu ɗari huɗu da ke wa wani jaminta, da ke yawo a kafofin sada zumunta.

Leave a Reply