Hukumar EFCC ta kama mutane 12 a Kano da Katsina bisa laifin sayen ƙuri’u

Hukumar yaƙi da yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta’annati, (EFCC) ta ce ta kama mutane 12 da ake zargi da sayan ƙuri’u a zaɓen da aka kammala ranar Asabar a jihohin Kano da Katsina.

Kwamandan hukumar EFCC na shiyyar Kano, Faruƙ Dogondaji ne ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya, a wata hira da ya yi da manema labarai cewa, an kama waɗanda ake zargin da tsabar kuɗi Naira miliyan 1.5 a jihohin Kano da Katsina.

A cewarsa, an kama mutane 10 ne a ƙaramar hukumar Doguwa ta jihar Kano, biyu kuma a ƙaramar hukumar Kankiya ta jihar Katsina.

KU KUMA KARANTA: Hukumar Kwastam ta Seme ta miƙawa EFCC dala miliyan 6 na bogi

Mista Dogondaji ya ce, an kama waɗanda ake zargin ne a lokacin da suke ƙoƙarin jawo waɗanda suka cancanta da kuɗi a wasu rumfunan zaɓe.

Ya ce an kama waɗanda ake zargin su 10 ne da Naira miliyan 1,357,500 a ƙaramar hukumar Doguwa, yayin da aka kama mutanen biyu da N242,000 a ƙaramar hukumar Kankia.

“Har ila yau, za mu kasance a duk cibiyoyin tattarawa sakamakon zaɓe don hana canjin sakamako,” in ji shi.

Ya ce kasancewar jami’an da ke gudanar da zaɓen zai ƙara sahihanci ga aikin. Kwamandan na EFCC ya ce za a gurfanar da waɗanda ake zargin a kotu bayan bincike.


Comments

One response to “Hukumar EFCC ta kama mutane 12 a Kano da Katsina bisa laifin sayen ƙuri’u”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Hukumar EFCC ta kama mutane 12 a Kano da Katsina bisa laifin sayen ƙuri’u […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *