Hukumar EFCC ta kama maɓoyar ‘Yahoo-Yahoo’ a Benuwe, ta kama mutane 14 da ake zargi

2
642

Jami’an Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati (EFCC) sun kama wasu mutane 14 da ake zargi da damfarar yanar gizo a Makurɗi, jihar Benuwe.

Kakakin hukumar ta EFCC, Wilson Uwujaren ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja A cewarsa, waɗanda ake zargin sun haɗa da Solomon Oloche, Innocent Ochola, Aselo Wisdom, Simon Jeff, Innocent Raphael, Akula Kelvin, Emmanuel Okanche, Francis Chikodirie, Atoo Michael, Ochayi Nelson, Ngutor Paul, Michael Tyobe, Samuel Okanche, da Patience Tseaa.

Ya ce an kama su ne bayan da aka gudanar da bincike kan wasu bayanan sirri da ake zarginsu da aikatawa.

KU KUMA KARANTA: EFCC ta gurfanar da Stella Oduah a kotu kan badaƙalar naira biliyan biyar

“Kayayyakin da aka ƙwato daga hannunsu sun haɗa da mota ƙirar Toyota Camry, iPhones 14, wayoyin Android 11, kwamfutocin Laptop 6, Katin ATM daban-daban, flash drive, MTN Router, Tus bike da wasu takardu masu laifi.

“Waɗanda ake zargin sun yi maganganu masu amfani kuma za a gurfanar da su gaban kotu da zarar an kammala bincike,” inji shi.

2 COMMENTS

Leave a Reply