Hatsarin mota ya ci rayukan mutane 5 a Yobe

0
177
Hatsarin mota ya ci rayukan mutane 5 a Yobe

Hatsarin mota ya ci rayukan mutane 5 a Yobe

Daga Shafa’atu Dauda Kano

Wani mummunan hadarin mota ya yi sanadiyar mutuwar fasinjoji biyar tare da jikkata wasu biyar.

Hadarin ya afkune a kusa da tashar mota ta Damagum a karamar hukumar Fune a jihar Yobe.

Wani Shaidar gani da ido, Abubakar Jajere ya ce hatsarin ya faru ne lokacin da direban motar bas mai kujeru sha takwas ya bugi bulo da yake tafiya a kan titi, daga bisani kuma ya rasa yadda zai yi da motar.

KU KUMA KARANTA:Mummunan hatsarin mota a Yobe, ya kashe mutane 10, uku sun jikkata

Ma’aikatan agajin gaggawa na jihar Yobe (Yemabus) sun yi gaggawar amsa kiran gaggawa tare da kwashe fasinjojin da suka mutu da wadanda suka jikkata zuwa babban asibitin Damagum, sannan kuma su ka daukesu zuwa asibitin koyarwa na jami’ar jihar Yobe Damaturu mai tazarar kilomita sittin daga wurin da hatsarin ya afku.

Leave a Reply