Hatsarin kwale-kwale ya kashe mutane 12 a jihar Nassarawa

3
205

Majalisar dokokin jihar Nasarawa ta ce mutane 12 ne suka mutu a wani hatsarin kwale-kwale a kogin Kogi Kungra Kamfani da ke gundumar Arikiya ta ƙaramar hukumar Lafiya ta jihar a ranar 20 ga watan Agusta.

Shugaban majalisar Ibrahim Abdullahi ne ya bayyana haka a wani zaman gaggawa da majalisar ta yi a ranar Alhamis a garin Lafiya.

Mista Abdullahi ya jajantawa ƙananan hukumomin jihar da na Lafiya bisa aukuwar lamarin. Ya kuma jajantawa iyalan waɗanda suka rasu bisa rasuwar ‘yan uwansu.

“Abin takaici ne matuƙa yadda muka rasa mutane 12 da suka haɗa da maza da mata a wani hatsarin jirgin ruwa a Arikiya da ke ƙaramar hukumar Lafiya.

“Mutane 19 ne ke cikin jirgin, 12 sun mutu sannan bakwai sun samu ceto. An jefa ƙaramar hukumar Lafiya da jiharmu cikin alhini kan wannan abin baƙin ciki da ya faru,” inji shi.

KU KUMA KARANTA: Hatsarin kwale-kwale ya hallaka mutum 76 a jihar Anambra

Majalisar wadda ta bayyana lamarin a matsayin abin takaici, sai dai ta buƙaci ‘yan uwa da al’ummar ƙaramar hukumar Lafiya da gwamnatin jihar da su ɗauki wannan rashi da ba za a iya kwatantawa ba.

“A madadina, ‘yan majalisu da ma’aikata, muna jajantawa iyalan mamatan, ƙaramar hukumar Lafiya da gwamnatin jihar bisa rasuwarsu.

“Muna addu’ar Allah ya hutar da rayukansu,” in ji kakakin. Ya kuma yi addu’ar Allah ya gafarta wa waɗanda abin ya shafa kurakuransu, ya kuma sa sun huta.

Daga baya ‘yan majalisar sun yi shiru na minti ɗaya domin girmama rayukan da suka rasu.

3 COMMENTS

Leave a Reply