Al’umomin garuruwan yammacin Zariya sun koka kan hauhawar hare-haren ‘yan-bindiga a yankin da su ka ce kullum sai an kashe musu mutane kuma a sace wasu don karɓar kuɗin fansa.
Al’umomi sun ce kullum sai sun bizne gawar mutanen da ‘yan-bindiga kan kashe, banda maganar miliyoyin kuɗin fansa.
Al’umomin garuruwan yammacin Zariya dai sun ce yanzu rayukan mutanensu bai zama komai ba gurin ‘yan-bindiga saboda yadda kusan kullum sai an kaiwa garuruwan hari.
Alhaji Ɗayyabu Kerawa wanda ya yi magana da yawun al’umomin yankin ya ce gaskiya tura ta kai bango.
Kafin yanzu dai an sami sauƙin hare-haren ‘yan-bindiga a wasu yankunan na jihar Kaduna, sai dai dawowar hare-haren ya sa masana harkokin tsaro irin su Manjo Yahaya Shinko mai-ritaya ke cewa akwai abubuwan lura musamman ganin yadda hare-haren ke ta ƙara hauhawa a wasu yankunan jihar Kaduna.
KU KUMA KARANTA:Ministar ma’aikatar kasuwanci ta Burtaniya ta iso Najeriya domin ziyarar kwanaki uku
Manjo Shinko ya ce akwai yuwuwar matakan da gwamnatocin Katsina, Zamfara da Sakkwato su ka ɗauka ne ya hana ‘yan-bindigan sukuni shi ya sa suka dawo cikin Kaduna.
Ƙoƙarin jin ta bakin jami’an tsaro dai ya ci tura saboda Muryar Amurka ta tura saƙo amma babu amsa har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.
Ko da yake gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani ya taɓa shaida mana matakan da gwamnati ke ɗauka, inda ya ce gwamnati ta haɗa kai da sarakuna da dagatai da masu unguwanni don tattara bayanan sirri sannan kuma gwamnatin tarayya za ta ƙarowa jihar Kaduna jami’an sojoji.
Hare-haren ‘yan-bindiga a waɗannan yankuna dai sun zo a daidai lokacin da ake fama da tsadar rayuwa saboda kuma mutane dayawa a yankin ba su yi noma ba saboda matsalar tsaro sannan sayen abinci kuma ya gagara saboda tsada.