Har yanzu akwai mutane 27 gurin yan garkuwan da jirgin ƙasa ya ratsa, ya kamata Buhari ya ƙara himma – Tukur Mamu

0
489

Jagoran tattaunawa da masu garkuwa da fasinjojin jirgin daga Abuja zuwa Kaduna, Malam Tukur Mamu, ya tabbatar da cewa sauran mutane 27 da harin jirgin ƙasa ya shafa na hannunsu.

Mamu, ya tabbatar da hakan ne a wata takardar manema labarai da ya sanyawa hannu a ranar Talata a Kaduna. Ya ce “wannan sheda ce don tabbatarwa ba tare da wata shakka ba cewa sauran fasinjoji 27 na harin jirgin ƙasa har yanzu suna hannun waɗanda suka sace su, kusan watanni 5 bayan afkuwar lamarin da za a iya hana faruwarsa”.

“Duk da cewa na nesanta kaina daga tattaunawar, ‘yan uwa da ‘yan jaridu da suka damu da ‘yan Najeriya sun yi ta kiraye-kirayen su tabbatar da gaskiyar labarin yayin da wasu da dama suka yi ta murna har ma da taya ‘yan uwan ​​waɗanda abin ya shafa murna,” in ji shi.

“Duk da dukkanmu muna addu’a da gaske don mu ji abin alkhaeri, yana da matukar rashin dacewa ga dillalan labarai na FAKE NEWS su yaɗa bayanan sirri waɗanda ba za a iya tantance su ba, sannan labaran da za su haifar da da damuwa a tsakanin ‘yan uwan waɗanda abin ya shafa, da duk wanda ya damu dasu, da kuma miliyoyin masu fatan alheri a duk faɗin duniya. “

“Har yanzu yanayin sauran waɗanda abin ya shafa ya yi muni sosai, da yawa daga cikinsu ba su da lafiya, damina ta yi musu yawa. Ina kira ga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da ya ƙara kaim wajen ganin an sako su cikin gaggawa, saboda halin da ake ciki yanzu, iyalan waɗanda har yanzu suke cikin dajin, kowace hanya ta gagara domin a yi sulhu da ‘yan uwansu lafiya”.

Leave a Reply