Hamas ta naɗa Yahya Sinwar a matsayin sabon shugaba

0
49
Hamas ta naɗa Yahya Sinwar a matsayin sabon shugaba

Hamas ta naɗa Yahya Sinwar a matsayin sabon shugaba

Ƙungiyar gwagwarmayar Falasɗinawa ta Hamas a ranar Talata ta naɗa Yahya Sinwar a matsayin sabon shugabanta na siyasa.

Sinwar zai maye gurbin Ismail Haniyeh, wanda aka kashe a Tehran bayan ya halarci bikin rantsar da sabon shugaban ƙasar Iran a ranar 31 ga watan Yuli.

Hamas da Iran sun zargi Isra’ila da kashe Haniyeh, amma Tel Aviv ba ta musanta ko tabbatar da alhakin hakan ba.

Sinwar dai shi ne shugaban Hamas da Isra’ila ke nema ruwa a jallo, inda Tel Aviv ta zarge shi da kitsa harin na ranar 7 ga watan Oktoba, wanda ya sa Isra’ila ta kaddamar da wani mummunan yakin soji a Zirin Gaza wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 39,600 tun daga ranar 7 ga watan Oktoban da ya gabata, a cewar hukumomin lafiya na ƙasar.

Watanni goma a cikin yakin Isra’ila, yankunan Gaza da dama sun zama kufai a cikin yanayin saka musu takunkumin shigar da abinci da ruwa mai tsabta, da magunguna.

KU KUMA KARANTA: An kashe shugaban Hamas, Ismail Haniyeh, a Iran

Ana tuhumar Isra’ila da aikata kisan kiyashi a kotun ƙasa da ƙasa, wacce ta ba da umarnin dakatar da kai hare-haren soji a kudancin birnin Rafah, inda Falasɗinawa sama da miliyan daya suka nemi mafaka daga yakin kafin a mamaye shi a ranar 6 ga watan Mayu.