Gwamnonin da suka fara takun saƙa da waɗanda za su gaje su tun kafin miƙa mulki

0
366

Wasu gwamnonin jihohi sun sha kaye a hannun manyan abokan hamayyarsu a zaɓen gwamnoni da membobin majalisun jihohi da aka kammala ranar 18 ga watan Maris, 2023.

Gwamnonin da hakan ta faru da su sun gama zangon mulkinsu na biyu na tsawon shekaru 8, amma duk da haka suka gaza samun amincewar mutanensu wajen tabbatar da ɗan takarar da suke so ya gaje su.

Bayan shan rashin nasara a zaɓen da ya gabata, gwamnonin sun fara samun matsala da zaɓaɓɓun gwamnonin da za su gaje su har an fara cece-kuce da nuna yatsa, har da zare idanu da murza gashin baki.

KU KUMA KARANTA: Takarar Gwamnan Zamfara: Ana Fargabar Jam’iyyar PDP Na Iya Rasa Damar Ta A Zaben 2023

Mafi yawan matsalolin da ke haɗa gwamnoni masu ci da masu jiran gadon faɗa sun shafi yanayin tafiyar da harkokin kuɗi na jihohi da wasu muhimman batutuwa.

Wasu daga cikin gwamnonin da muka tattaro muku sun ƙunshi, Abdullahi Ganduje na jihar Kano, Samuel Ortom na jihar Benuwai da Okezie Ikpeazu na Abia.

Gwamna Ortom na jihar Benuwai

Gwamna mai barin gado a jihar Benuwai, Samuel Ortom, na PDP ya fara fuskantar ƙalubale daga zaɓaɓɓen gwamna mai jiran gado, Hyacinth Aliya, na APC, kamar yadda jaridar Vanguard ta rawaito.

Manyan mutanen biyu sun fara nuna wa juna yatsa ne bayan wani kundi ya sulalo ya fito wanda zaɓaɓɓen gwamna ya aike wa shugaban kamfanin zuba hannun jari na Benuwai (BIPC), Alex Adum.

Gwamna Ikpeazu na Abia

Gwamna mai barin gado na jam’iyyar PDP a Abia, Okezie Ikpeazu, yanzu haka ya fara takun saƙa da zaɓaɓɓen gwamna na Labour Party, Alex Otti, inda shi kuma ya gargaɗe shi ya daina sa ka baki a gwamnatinsa.

A makon da ya shige, babbar kotun tarayya a Abuja ta garkame wasu asusunan banki mallakin jihar, lamarin da gwamna Ikpeazu ya zargi Otti da kulla manaƙisa.

Leave a Reply