Gwamnatina za ta ba da fifiko kan walwalar mata-Tinubu

0
140

Shugaban ƙasar Najeriya, Bola Tinubu, ya sha alwashin cewar gwamnatinsa za ta ba da fifiko kan walwalar mata da kiyaye haƙƙoƙinsu tare da bunƙasa rayuwarsu.
A sanarwar da hadiminsa akan harkokin yaɗa labarai, Ajuri Ngelale ya fitar game da zagayowar ranar mata ta duniya, Tinubu ya bayyana mata a matsayin ƙashin bayan ci gaban kowace al’umma.

Shugaban ƙasar wanda ya fayyace irin rawar da mata ke takawa wajen gina al’umma, ya jaddada cewar, babu shakka, matan Najeriya sun ba da gudunmowa wajen bunƙasa, ci gaba da kuma ɗaukakar ƙasar.

KU KUMA KARANTA:Gwamnatin Najeriya za ta fara amfani da kimiyyar zamani wajen fuskantar ‘yan bindiga

A cewar sanarwar, “Shugaba Tinubu ya ba da tabbacin cewar a kowane ɓangare na ci gaban ɗan adam, irin zarar da matan Najeriya suka yi shaida ce ta jajircewa da ƙarfin hali da fikira ta dukkanin matan duniya, kuma wata alama ce ta nagartaccen wakilci na kyakkyawan fata da wanzuwar al’amura.

Tinubu ya ƙara da cewar, taken bikin ranar mata ta duniya na bana na, “a zuba jari a mata domin hanzarta ci gaba”, ya dace da manufofin da gwamnatinsa ta ƙirƙira akan ilimi da baiwa mata tallafi, ba wai kawai ta hanyar shigo da su a harkar mulki ba, harma da tabbatar da cewa sun ci gaba da zama murya mai mahimmanci a fannin ci gaba a dukkanin ɓangarorin tattaliin arziƙi.

Hakazalika Shugaba Tinubu yace, “gwamnatinsa ta maida hankali wajen zuba jari a fannin ilmin ‘ya’ya mata, tare da ƙirƙirar tsare-tsaren da za su ƙarfafesu wajen ba da gudunmowa a fannonin ilmi da kimiya da fasaha da bincike da ƙirƙire-ƙirƙiren da za su yi tasiri a nan gaba”.

Leave a Reply