Gwamnatin Katsina za ta kafa asibitoci 361 – Gwamna Raɗɗa

2
340

Gwamna Dikko Raɗɗa na jihar Katsina ya bayyana shirin gwamnatin sa na kafa ƙananan Asibitoci na kar-ta-kwana guda 361 domin inganta harkokin kiwon lafiya a jihar.

Gwamna Raɗɗa ya bayyana haka ne a lokacin da yake ƙaddamar da rabon babura 198 ga jami’an rigakafi na yau da kullum da masu kula da unguwanni.

Ya ce za a kafa asibitocin kafin ƙarshen wa’adinsa a faɗin ƙananan hukumomin jihar 34.

KU KUMA KARANTA: Katsina za ta ɗauki sabbin malamai dubu bakwai

Shirin, in ji shi, wani ɓangare ne na ƙudirinsa na inganta samar da ingantattun ayyukan kiwon lafiya a matakin farko.

Ya ce rabon babura ne da nufin inganta harkar rigakafi da sauran ayyukan kiwon lafiya a matakin farko a jihar.

“Na jajirce sosai wajen ƙarfafa fannin lafiya domin cimma muradun al’ummar jihar Katsina.

“Haka kuma, mun sadaukar da kai don inganta ayyukan kiwon lafiya ga ‘yan ƙasa,” in ji shi.

Gwamnan ya buƙaci al’umma da malaman addini da sauran masu ruwa da tsaki da su wayar da kan al’ummarsu kan mahimmancin tallafin kiwon lafiya.

Ya kuma umarci jami’an rigakafi da jami’an tsaro da su tabbatar da yin amfani da baburan yadda ya kamata wajen gudanar da ayyukansu.

Tun da farko, Dakta Ahmed Tijjani Hamza, Babban Sakatare na Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Katsina, ya yaba wa Gwamnan bisa yadda ya jagoranci ajandar sake fasalin kiwon lafiya, don inganta samar da ayyuka masu inganci.

Ya ce shirin zai cimma manufofinsa tare da tallafawa abokan hulɗar ci gaba.

2 COMMENTS

Leave a Reply