Gwamnatin Katsina ta jaddada manufarta na ci gaba da bayar da horo ga malaman makaranta

0
57
Gwamnatin Katsina ta jaddada manufarta na ci gaba da bayar da horo ga malaman makaranta

Gwamnatin Katsina ta jaddada manufarta na ci gaba da bayar da horo ga malaman makaranta

Daga Idris Umar, Zariya

Kwamishinar kula da ilimin firamare da na Sakandire ne ta bayyana ƙudirin gwamnatin jihar mai ci yanzu na ci gaba da bayar da ƙarin horo ga malamai a faɗin jihar don samar da ƙwararrun malamai da suka iya sarrafa na’ura mai ƙwaƙwalwa da za su yi gogayya da takwarorinsu a faɗin duniya.

Hajiya Zainab Musa Musawa ta bayar da tabbacin hakan ne a lokacin da ta kai ziyarar duba yadda shirin horar da malamai 10,000 da suka haɗa da sabbin ɗauka 7,000 a kan dabarun koyarwa na ƙarni na 20 ke gudana.

Kwamishinar ta kai ziyarar ne a makarantar firamare ta Modoji inda ake gudanar da bayar da horon na yini 3 wanda Ma’aikatar kula da ilimin firamare da na Sakandire, hukumar ilimin bai ɗaya da kuma haɗin gwiwa da shirin bunƙasa ilimi matakin jiha (TESS) suka shirya.

KU KUMA KARANTA: Da ilimi ake samun kowace irin nasara a rayuwa – Dauda Lawal 

Hajiya Zainab Musa Musawa wanda ta zagaya azuzuwa ta kuma tattauna da masu bayar da horon da Kuma malaman, ta bukace su da suyi amfani da lokacin su fahimci Abunda aka koyamasu don bunkasa tsarin koyo da koyarwa a jihar.

A yayin ziyarar dai Kwamishinar ta samu rakiyar Babbar Sakatariya a Ma’aikatar Hajiya Mairo Mohamed Othman, Mai baiwa Gwamna shawarma akan ilimi Nura Sale Katsayal sauran Daraktocin Ma’aikatar.

Bayanin hakan na ƙunshe a cikin wata sanarwa wadda jami’in hudda da jama’a na Ma’aikatar Malam Sani Ɗanjuma Suleiman ya Sanyama hannu a katsina.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here