Gwamnatin Kano zata rufe duk gurin da ba a karɓar tsohon kuɗi

2
368

Daga Shafa’atu DAUDA, Kano

Shugaban Hukumar kula da Zirga-zirgan ababen hawa a jihar Kano (KAROTA) Baffa Babba Dan’agundi ya bayyana cewa gwamnatin jihar zata rufe duk wuraren da basa karɓar tsohon kuɗi.

Ya ce tuni Gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ya bayar da umurnin rufe duk wani gurin kasuwance a faɗin jihar wanda yaƙi karbar tsofaffin kuɗi

Baffa Babba ya ce an ɗauki matakin ne saboda ƙorafe-korafen jama’a da ya yi yawa na ƙin karɓar tsofaffin kuɗin a hannun jama’a musamman a wasu daga cikin gidajen mai da asibitoci da wajen saye da sayarwa na faɗin jihar nan

Hakan ya biyo bayan umarnin da babban bankin ƙasa CBN ya bayar na ci gaba da karbar tsofaffin kuɗin.

KU KUMA KARANTA: Yadda ƙarancin naira ya haddasa rikici a Ogun

Tuni dai Gwamna ya bayar da umurni ga kwamitin kar-ta-kwana mai kula da gidajen mai su fita su tabbatar ana karɓar tsofaffin kuɗin.

Ya bayyana cewa duk wanda yaƙi bin umarnin ya saɓa da dokar hukumar kula da haƙƙin mai saye da sayarwa ta Consumer Protection Council, sashe na 10 ƙaramin sashi na 1(b) da kuma sashe na 10 ƙaramin sashi na 2 na dokar hukumar.

Ya ƙara da cewa duk wanda aka kama za a rufe wajen kasuwancinsa tare da gurfanar da shi a gaban shari’a domin daukar mataki na gaba.

2 COMMENTS

Leave a Reply