Gwamnatin kano ta haramta zirga zirgar adaidaita sahu daga 10 na dare zuwa 6 na safe

0
252

Daga Fatima GIMBA, Abuja

Gwamnatin Jihar Kano ta bada sanarwar haramta ayyukan baburan Adaidaita sahu daga ƙarfe 10:00 na safe har zuwa ƙarfe 6:00 na wayewar gari. Dokar zata fara aiki ne daga ranar alhamis 20 ga wata Juli, Shekara ta 2022.

Jawabin na ƙunshe ne a cikin sanarwar da Kwamishinan Ma’aikatar yaɗa labaran Jihar Kano Malam Muhammad Garba ya fitar, wadda ta nuna cewa an dauki wannan mataki alokacin zaman Majalisar harkokin tsaron Jihar ta Kano.

Yace ɗaukar wannan mataki na cikin ƙoƙarin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar Jihar Kano.

A cikin jawabin, Kwamishinan ya buƙaci matuƙan baburan Adaidaita sahun da suyi ƙoƙarin bin wannan doka kamar yadda doka ta tsara lokacin amfani da baburan domin Jami’an tsaron zasu tabbatar da  aiki da wannan doka ba tare da bata lokacin ba.

Leave a Reply