Gwamnatin jihar Anambra ta dakatar da shugaban ƙaramar hukama saboda mutuwar matarsa

0
545

Daga Fatima GIMBA, Abuja

Gwamnatin jihar Anambra ta dakatar da Mbazulike Iloka, sabon shugaban kwamitin riƙon ƙwarya na ƙaramar hukumar Nnewi ta Arewa (LGA) bisa rasuwar matarsa, Chidiebere, a ranar Lahadi, 7 ga watan Agusta, 2022.

An sanar da hakan ne a wata wasika mai kwanan watan Agusta, 11, 2022 kuma kwamishinan ƙananan hukumomi, masarautu da al’amuran al’umma, Tonycollins Nwabuwanne ya sanyawa hannu.

A cewar wasikar, dakatarwar Iloka ya zama dole saboda yanayin mutuwar matarsa ​​da kuma bada damar kammala bincike.

Takardar dakartarwar

Wani ɓangare na wasikar yana cewa: “Bayan baƙin cikin da rasuwar matarka, marigayiya Misis Chidiebere Iloka, a ranar 7 ga watan Agusta, 2022, an yi ta cece-kuce a tsakanin jama’a kan lamarin da ya yi sanadin mutuwarta, ciki har da zargin da ake yi mata yiwuwar kisan kai.

“Yayin da ake zaton ba ka da laifi har sai an kammala bincike, ya zama wajibi ka koma gefe don ba da damar gudanar da bincike da adalci.”

Leave a Reply