Gwamnatin Jigawa ta kori Alkalin kotu kan karɓar cin hanci

0
400
Ta kama mijinta yana lalata da ’ya’yan cikinsu

Hukumar da ke kula da harkokin shari’a ta jihar Jigawa ta umarci Alƙalin kotun shari’a, mai shari’a Safiyanu Muhammad da ya ajiye aikinsa, saboda karɓar cin hancin Naira dubu hamsin (N50,000) daga hannun wani mai ƙara.

Duk da cewa daraktan yaɗa labarai da ƙa’ida na ma’aikatar shari’a ta jihar, Abbas Rufa’i, bai fayyace irin laifin da Alƙalin ya aikata ba, amma jaridar DAILY NIGERIAN ta tattaro cewa an bincike shi tare da gurfanar da shi a gaban kotu bayan da mai shigar da ƙara ya shigar da ƙara a kansa kan karɓar Naira dubu 50,000 cin hanci a hanunsa.

“Hukumar ta haɗa baki ta yanke hukuncin cewa dole Alƙali Safiyanu Muhammad ya ajiye aikinsa bisa laifin aikata laifin a lokacin da wani mai ƙara ya gurfana a gabansa a wata kotun Shari’ar Musulunci da ke Birnin Kudu,” in ji Malam Rufa’i a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar.

KU KUMA KARANTA: Kotu ta umarci wani magidanci da ya yanka zakaransa, saboda ya taƙura wa makwabta

Sai dai hukumar ta gargaɗi ma’aikatanta da su guji duk wani nau’i na cin hanci da rashawa domin a tsaftace ɓangaren shari’a a jihar.

Don haka ta ƙara da cewa hukumar ta sake jaddada aniyar ta na tunkarar duk wani ma’aikaci da aka samu yana so a sauke aikinsa a hukumance.

Hukumar ta kuma naɗa wasu manyan ma’aikatan hukumar su huɗu, a muƙamai daban-daban. Sanarwar ta ce, an yanke wannan shawarar ne a yayin taro karo na 170 na hukumar kula da harkokin shari’a ta jihar da aka gudanar a birnin Dutse na jihar Jigawa a ranar Alhamis.

Haka kuma, hukumar ta yanke shawarar naɗa Aliyu Mohammed a matsayin mataimakin magatakarda na biyu na kotun ɗaukaka ƙara ta shari’a da kuma Abdulrashid Alhassan a matsayin babban sufeto na kotun ɗaukaka ƙara ta shari’a.

Sauran sun haɗa da Muhammad Lawan a matsayin mataimakin babban sufeto na shiyyar, kotun ɗaukaka ƙara ta shari’a da Muhammad Adamu mataimakin babban sufeto na shiyyar kotun ɗaukaka ƙara ta shari’a.

A halin da ake ciki, bisa ga dokar da ta kafa hukumar da aikinta, ƙungiyar Alƙalan kotunan shari’ar Musulunci ta Jihar Jigawa, JISSJA, ta yaba wa hukumar bisa wannan nasarar da ta samu tare da ba ƙungiyar tabbacin goyon bayansu da haɗin kai.

Leave a Reply