Gwamnatin Isra’ila ta yanke shawarar rufe duka ofisoshin Al Jazeera a ƙasar

0
93

Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu a ranar Lahadi ya bayyana cewa gwamnatinsa ta yi ƙuri’a inda ta amince ta rufe duka ofisoshin kafar watsa labarai ta Al Jazeera a ƙasar.

Netanyahu ne ya sanar da hakan a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, sai dai bai bayyana sauran bayanai da suka ƙunshi ko yaushe dokar za ta soma aiki ba haka kuma babu bayani kan rufewar ta har abada ce ko da wucin-gadi ce.

Har ila yau, Isra’ilar ta yi barazanar saka ƙafar wando ɗaya da Qatar, wadda ke da tashar, a daidai lokacin da gwamnatin ta Doha ke taka muhimmiyar rawa a ƙoƙarin shiga tsakani domin dakatar da yaƙin Gaza.

KU KUMA KARANTA: Jami’an Isra’ila sun kai samame ofishin Al Jazeera a Birnin Ƙudus

Isra’ila ta daɗe tana rashin jituwa tsakaninta da Al Jazeera, inda ta zarge ta da nuna son kai ga al’ummar ƙasar.

Al Jazeera na ɗaya daga cikin kafafen yaɗa labarai na ƙasa da ƙasa da ke ci gaba da zama a Gaza a tsawon yakin da ake yi, inda suke yaɗa hotunan zubar da jini na hare-hare ta sama da cunkoson asibitoci tare da zargin Isra’ila da kisan kiyashi.

Haka kuma Isra’ilar na zargin Al Jazeerar da haɗa kai da abokiyar gabarta wato Hamas.

Leave a Reply