Gwamnatin da Netanyahu ke jagoranta na cikin tsaka-mai-wuya — Bayanan sirrin Amurka

0
133

Jami’an leƙen asirin Amurka sun yi gargaɗin cewa mai yiwuwa gwamnatin Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu na cikin tsaka-mai-wuya” a lokacin da jama’a ke ƙara ƙosawa da shugabancinsa.

“Ɗorewar Netanyahu a matsayin shugaba da kuma jami’iyyun haɗakar gwamnatinsa mai tsattsauran ra’ayi da suke aiwatar da tsauraran manufofi kan Falasɗinawa da batun tsaro, suna cikin tsaka mai wuya,” a cewar wani rahoto na Ofishin Daraktan Tsaron Cikin Gida (ODNI) a ranar Litinin.

“Rashin amincewa kan iya jagorancin Netanyahu na ƙara faɗaɗa a cikin jama’a daga matakin da take kafin yaƙi, kuma muna zaton za a gudanar da gagarumar zanga-zangar neman yin murabus ɗinsa kafin zaɓe.

“Akwai yiwuwar samun wata gwamnatin mai sassaucin ra’ayi,” kamar yadda sanarwar ta yi ƙarin bayani.

KU KUMA KARANTA: Ministocin Isra’ila sun yi tir da kuɓutar da marayu da dama daga Gaza da aka yi wa ƙawanya

Rahoton na hukumomin leƙen asirin na Amurka, wanda ya dogara ne kan bayanan da aka samu daga 22 ga watan Janairu, ya ƙara da cewa “watakila Isra’ila ta ci gaba da fuskantar turjiya da makamai daga Hamas nan da wasu shekaru masu zuwa.”

Ta ƙara da cewa sojoji “za su yi fafutukar” lalata hanyoyin ƙarƙarshin ƙasa na Hamas.”

Hukumomin na leƙen asiri sun tabbatar da cewa shugabannin Iran “ba su suka shirya, sannan ba su da masaniya kan” tsallaka iyaka da harin da Hamasa ta kai wa Isra’ila ranar 7 ga Oktoba.

Hukumomin asirin sun kuma yi gargaɗin cewa yiwuwar fantsamar rikicin zuwa ƙasashe maƙwabta “na da matuƙar karfi.”

Yaƙin da Isra’ila ta ƙaddamar kan Falaɗinawa a Gaza — a yanzu da ya shiga rana ta 159 — ya kashe aƙalla mutum 31,185, mafi yawancinsu ƙananan yara da mata, sannan ya jikkata mutum 72,889.

Leave a Reply