Gwamnan Zamfara Bashi Da Hannu A Batun Kokarin Tsige Mataimakinsa – Shinkafi

0
659

Daga; IMRANA ABDULLAHI.

MAI ba Gwamnan Jihar Zamfara shawara a kan harkokin hulda da kasashen waje Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi, ya bayyana cewa Gwamna Matawalle bashi da hannu a batun kokarin da majalisar dokokin Jihar Zamfara ke yi domin Tsige mataimakinsa Mahadi Aliyu Gusau.

Dokta Suleiman Shinkafi ya ce hakika Gwamnan Jihar Zamfara ba wannan maganar ce a gabansa ba, don haka mutane su daina danganta shi da wannan maganar.

“Abin da ke gaban Gwamnan Zamfara kawai batu ne na yaya za a samu zaman lafiya a Jihar Zamfara a daina kashe Jama’a haka nan kawai ba gaira ba dalili, amma ba batun mataimakinsa ba wannan batun ma ba ya gabansa ko kadan”, inji tsohon Sarkin Shanun Shinkafi

“Majalisar dokoki ce ke yin wannan kokarin Tsige mataimakin Gwamnan Zamfara kuma su na da yancin yin hakan, saboda mataimakin Gwamnan ya daina zuwa ofishinsa da yakamata a rika zuwa domin gudanar da aiki, amma sai ya yi watanni baya zuwa ofishin nasa”, inji Dokta S. Shinkafi.

Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi ya kuma yi kira ga Gwamnatin tarayya da ta bayar da wadansu kudi na musamman ga Jihohin da ke fama da wannan matsalar ta tsaro wanda suka hada da Jihar Zamfara kasancewarta jiha ce da ba ta da wani kudin shiga, sai kudin daunin da ke shigowa na wata wata daga Gwamnatin tarayya.

Sai ya bayyana Gwamna Bello Muhammad Matawalle a matsayin wanda ke kokarin tabbatar da zaman lafiya a koda yaushe, mai hakuri da hangen nesa.

Leave a Reply