Gwamnan Ondo, ya kori mambobin majalisar zartarwar jihar, ya ba da umarnin su miƙa iko ga sakatarorin dindindin

0
135

Daga Maryam Umar Abdullahi

An umurci dukkan mambobin majalisar da su gaggauta miƙa su ga sakatarorin dindindin ko kuma babban jami’in gudanarwa a ma’aikatunsu.

Gwamnan jihar Ondo Lucky Aiyedatiwa ya rusa majalisar zartarwa jihar ne a ranar Laraba.

Mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Ebenezer Adeniyan, ya bayyana haka a Akure, inda ya ce ta hanyar rugujewar, dukkan mambobin majalisar za su miƙa su ga manyan sakatarorin dindindin ko kuma babban jami’in gudanarwa a ma’aikatun su.
Ya ƙara da cewa sauran waɗanda aka naɗa a siyasance kamar manyan mataimaka na musamman da masu taimaka wa gwamna suma an sauke su daga naɗin nasu.

KU KUMA KARANTA: Yaron gida ya faɗi, ya mutu, bayan uwargidansa ta tilasta shi ya yi lalata da ita

“An umurci dukkan jami’an da abin ya shafa da su miƙa duk kadarorin gwamnati da ke hannunsu.

“Gwamnan ya godewa jami’an da abin ya shafa saboda aiyuka da kuma gudunmawar da suke bayarwa wajen ci gaban jihar Ondo,” in ji Adeniyan.

Aiyedatiwa ya zama gwamnan jihar Ondo ne a ranar 27 ga watan Disamba bayan rasuwar tsohon shugaban sa, tsohon gwamnan jihar, Rotimi Akeredolu.

Leave a Reply