Gwamna Abba ya ƙaddamar da kwamitocin bincike kan rikicin siyasa da ta’annati da dukiyar Kano

0
149

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya ƙaddamar da kwamitocin biyu da za su yi bincike kan ta’annati da dukiyar al’umma, da mutanen da suka bata da rikicin siyasa da suka afku a tsakanin 2015 da 2023.

A yayin da yake ƙaddamar da kwamitocin a ranar Alhamis, Gwamna Yusuf ya yi alkawarin hukunta duk wanda aka samu da laifi.

Wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ta ambato Gwamna Yusuf yana tunatar da cewa bincike kan ta’annati da dukiyar al’umma wani bangare ne na alkawarin da ya yi a lokacin da ake rantsar da shi.

Ya ƙara da cewa za a binciko tare a hukunta masu hannu a rikicin siyasa a jihar Kano musamman a zaɓukan 2023.

Sanarwar ta ruwaito gwamnan na cewa “Rikicin siyasa babban ƙalubale ne ga dimokuraɗiyya a duniya baki ɗaya. Yana janyo asarar rayuka da dukiya, da ma janyo al’umma su ki amincewa da wadanda ke jagorantar su.”

“Munanan kashe-kashen da aka yi na siyasa musamman a 2023 ba za su tafi haka kawai ba, za a dauki matakin ne don hana afkuwar hakan a nan gaba,” a cewar gwamnan.

Kwamitin farko wanda yake karkashin Mai Shari’a Zuwaira Yusuf zai mayar da hankali kan rikicin siyasa da mutanen da suka bata tun daga 2015 zuwa 2023.

KU KUMA KARANTA: An haramta shirya fina-finan da ke nuna ƴan daudu da ƴan daba a Kano

Gwamna Abba ya ce “Muna sa ran za su binciki munanan ayyukan, sannan su zakulo wadanda suke daukar nauyin rikicin. Su nemo tushen rikicin, sannan su gano yadda aka kitsa rikici a 2015, 2019 da 2023.”

Da yake ƙaddamar da kwamiti na biyu ƙarƙashin Mai Shari’a Faruk Lawan, Gwamna Abba ya dora wa kwamitin alhakin gudanar da bincike kan ta’annati da dukiya da kadarorin al’umma.

Munanan kashe-kashen da aka yi na siyasa musamman a 2023 ba za su tafi haka kawai ba, za a dauki matakin ne don hana afkuwar hakan a nan gaba

Ya bukaci Ma Shari’a Lawan da dukkan mambobinsa kan kada su yi shayin bayyana duk wani waje da aka yi almundahana da dukiya ko ƙadarar al’ummar a lokacin mulkin gwamnatin da ta gabata a ciki da wajen jihar Kano.

Gwamnan ya kuma jaddada cewa wannan mataki ba shi da alaka da siyasa ko nufar wasu mutane, aiki ne da ya dace da buktun jama’ar jihar Kano.

A yayin da yake kira ga kwamitocin da kar su kuskura su hada baki da wani, Gwamnan na Kano Yusuf ya kuma bukace su da su riƙe amana da aiki da rantsuwar da suka yi ta gudanar da aiki da gaskiya don yin adalci a jihar.

Gwamnan ya ce sai da aka yi tantancewa sosai kafin a zaɓi mambobin kwamitocin, kuma ya yi amanna za su yi aikin kamar yadda ake zato.

Ya ce “Mun yi duba ga tarihin ayyukanku, kuma ba mu samu wani daga cikin ku da rashin kirki ba. Mun amince da ku kuma muna fatan za ku mika rahotanninku a cikin watanni uku.”

Leave a Reply