Gobara ta laƙume kadarorin naira miliyan 360 a Kwara

0
182

Wata gobara da ta tashi a safiyar ranar Talata ta ƙone shahararriyar Kasuwar Owode da ke Ƙaramar Hukumar Offa a Jihar Kwara.

Da yake tofa albarkacin bakinsa kan lamarin, kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, Hassan Adekunle, ya ce sun samu kiran neman ɗaukin gaggawa da misalin ƙarfe 2:30 na tsakar dare.

Ya ce, binciken da aka gudanar ya nuna cewa gobarar ta tashi ne sakamakon ɓarɓashin taba sigari da ta faɗo kan kayan da suke saurin ƙonewa.

“A kiyasi da kuma bincike farko da aka gudanar ya nuna cewa shaguna 50 ne suka ƙone daga cikin shaguna 3,820 da ke kasuwar.

“Darajar kayayyakin da kadarorin da aka ceto a ƙoƙarin kashe gobara an yi kiyasin sun haura Naira biliyan 12 yayin da aka yi asarar dukiya ta sama da Naira miliyan 360,” inji shi.

KU KUMA KARANTA: An yi asarar dukiya ta miliyoyin naira, sakamakon gobarar da ta tashi a kasuwar Idumota ta Birnin Legas

Adekunle ya ce Daraktan hukumar, Prince Falade John, ya jajanta wa ’yan kasuwar da suka yi asara da ɗaukacin al’ummar kasuwar.

Ya shawarci ‘yan kasuwa da su kasance masu taka-tsan-tsan da kuma kula da harkokin tsaro a kowane lokaci.

A baya an samu ɓarkewar gobara a kasuwar, wadda ta kasance ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin kasuwanci a jihar.

Leave a Reply