Gidauniyar MJ Alƙali ta raba wa marayu 100 kayan Sallah a Yobe (Hotuna)

0
259
Gidauniyar MJ Alƙali ta raba wa marayu 100 kayan Sallah a Yobe (Hotuna)

Gidauniyar MJ Alƙali ta raba wa marayu 100 kayan Sallah a Yobe (Hotuna)

Daga Ibraheem El-Tafseer

Gidauniyar jin ƙai da tallafawa marayu da marasa ƙarfi mai suna ‘MJ Alƙali Orphanage Foundation’ ta raba wa marayu 100 da ‘ya’yan marasa ƙarfi kayan Sallah. Taron raba kayan ya gudana ne ranar Lahadi da ta gabata, a unguwar bayan gidan Sarkin Potiskum, a jihar Yobe.

Hajiya Maimuna Jibrin Alkali ita ce shugabar wannan gidauniya, ta shaidawa Neptune Prime cewa, “duk da wannan shi ne karo na farko da muka fara rabon kayan sallah a marayu, gajiyayyu da marasa ƙarfi. Amma babban abin da ya ja hankali na, na yi wannan shi ne ganin yadda ubangidanmu Sanata Ibrahim Mohammed Bomoi (Sanata mai wakiltar Yobe ta Kudu) ya ke ta tallafawa mutane da masu ƙananan ƙarfi da marayu.

Ni ma wannan ne ya sa na ce tun da akwai talakawa marasa ƙarfi da marayu a kusa da mu, zan tallafa musu da kayan sallah ko da babu yawa. Kuma Alhamdulillah mun bi hanyoyin da suka da ce wajen tattaro waɗannan marayu da marasa ƙarfi su 100. Na saka an binciko min yara biyar a kowace unguwa a cikin garin Potiskum, ba wai a iya ‘yan unguwa ɗaya muka raba kayan ba.

Kuma da kuɗi na na yi wannan aiki, ba wai ba ni aka yi na raba ba. Kawai na ga halin da ‘ya’yan marasa ƙarfi da marayu suke ciki ne, kusan kowa zai yi adon Sallah amma ban da su, to wannan shi ya ƙara min ƙarfin guiwa na tallafa musu don su ma su yi fitar sallah cikin farin ciki.

KU KUMA KARANTA:Gidauniyar Ɗangote ta ƙaddamar da rabon abinci na naira biliyan 16 ga talakawa

Sannan ina ƙira ga gwamnati ta faɗaɗa, tallafin da take raba wa al’umma, ana zaƙulo irin waɗannan yara ana saka su a ciki. Don tabbas suna cikin mummunan hali.

Sannan ina ƙira ga gwamnati da a taimaka mana da ‘Solar’ a unguwar bayan gidan Sarkin Potiskum, Alhaji Umaru Bubaram, jikin gonar Sarki. Rashin hasken solar ɗin ya sa ɓarayi suna tare mata, sannan suna ƙwacen waya da kuɗaɗe a hannun jama’a. Inji ta.

Leave a Reply