Daga; MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI.
A KOKARIN ganin an taimakawa marasa lafiya da ke jinya a asibitin Dan-tsoho da ke cikin garin Kaduna ya sa Gidauniyar taimakawa marayu ta Amatullah karkashin jagorancin shugabarta Malama Hauwa’u Abubakar, tare da ma’aikatan gidauniyar Maza da mata da kuma Rakiyar manema labarai sun kai taimakon abincin bude baki domin taimakawa marasa lafiya da masu aikin kula da jinyarsu.
Za dai a iya cewa wannan Gidauniyar ta yi ko yi ne da irin kiraye-kirayen da ake yi wa masu wadata da su rika tunawa da marasa lafiya da ke kwance a asibiti suna neman lafiya, wanda hakan ya yi karanci a cikin al’umma.
Da misalin karfe 5: 45 na Yammacin ranar Asabar ne gidauniyar Amatullah karkashin jagorancin shugaba Hauwa’u Abubakar, suka Isa asibitin Dan-tsoho da ke cikin garin Kaduna dauke da kayan abincin da suka hada da Kunun Gero, Lemun sha mai kawo, ruwan sha da Alale, inda bisa Rakiyar wasu ma’aikatan asibitin aka rika shiga dakunan da marasa lafiya da masu jinyarsu ke ciki ana bi Gado Gadon marasa lafiya ana gaishesu ana kuma ajiye masu abincin da aka kawo masu Gwanin ban sha’awa su na cikin garin ciki da annashuwa da har wannan Gidauniya ta ‘Amatullah Orphanages Foundatiin” ta tuna da su.
Ita dai gidauniyar Amatullah na aikin taimakawa marayu da masu bukatar taimako ne musamman marasa lafiya da ba su da karfi, saboda kamar yadda wakilinmu ya samu bayani cewa ko a kwanan baya ma sai da Gidauniyar ta taimaka wa marasa lafiya da magani kala-kala.
Mun kuma ganewa idanun mu a harabar asibitin sai da aka samu wata mata rike da takardar da aka rubuta masu ta maganin da za su sayo amma kamar yadda aka Sani sakamakon halin yau sai gidauniyar ta taimaka wa matar da maganin da aka rubuta masu domin ba su da kudin sayen maganin.
Allah ya taimaka